Fulani Makiyaya: An Kashe Rayuka, An Kona Gidaje a Harin Ramuwar Gayya a Taraba

Fulani Makiyaya: An Kashe Rayuka, An Kona Gidaje a Harin Ramuwar Gayya a Taraba

  • Wasu matasa a ƙaramar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba sun karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, abin da ya janyo rikici da kisa
  • Rikicin ya fara ne bayan wani harin da wasu matasa suka kai wa makiyaya, wanda ya janyo ramuwar gayya da asarar rayuka da ƙone gidaje
  • An ce jami'an tsaro na shirin ƙaddamar da dokar hana fita domin hana ƙarin rikici da dawo da doka da oda a yankin da abin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Bayan makonni kaɗan da jami’an tsaro suka sasanta manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba, rikici ya sake ɓarkewa.

An ruwaito cewa lamarin ya janyo asarar rayuka da rushewar ƙoƙarin zaman lafiya da aka fara a yankin.

Taraba
An kai harin ramakon gayya a jihar Taraba. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Rahoton da mai bincike kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga harin da wasu matasa suka kai wa Fulani makiyaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ji cewa matasan sun kai hari wa Fulanin da ke kiwo a kusa da gonakinsu a yankin Badanwa, duk da gargaɗin da jami’an tsaro suka rika bayarwa.

An gudanar da taro sau uku tsakanin jami’an tsaro da shugabannin al’umma da matasa domin hana tashin hankali, amma duk da haka an karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma.

Yadda rikicin Taraba ya samo asali

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Juma’a, 23 ga Mayu, da misalin ƙarfe 2:50 na rana, wasu Fulani makiyaya sun kai harin ramuwar gayya bayan wani hari da suka ce matasa sun kai musu.

An samu rahoton cewa an kashe mutum biyu daga kauyen Munga Lelau, inda aka ce an sare su da adda yayin da rikicin ke ci gaba.

Bayanai da Legit ta samu sun nuna cewa jami’an tsaron Operation Lafiyan Jama’a sun isa wurin domin shawo kan lamarin.

Sojoji
Sojoji sun kashe mutum 2 a harin Taraba. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Lokacin da sojoji suka bi diddigin lamarin, sun ci karo da wasu ‘yan bindiga da ke ƙone gidaje a Munga Lelau.

An kashe mutum biyu daga cikinsu, an kuma kwato bindigar gida, wayar hannu, da harsasai guda huɗu.

An karya yarjejeniyar zaman lafiya a Taraba

Jami’an tsaro sun bayyana da matasan sun bi shawarar shugabanni da na hukumomi da ba a samu rikicin ba.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce:

"Mun riga mun shimfiɗa tsarin sulhu amma wasu sun zaɓi tada zaune tsaye,”

Ana hasashen saka dokar hana fita a Taraba

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun ƙara tsaurara sintiri a yankunan da rikicin ya auku domin hana sake ɓarkewar tashin hankali.

An ba da shawarar cewa gwamnatin ƙaramar hukumar ta sanya dokar hana fita a yankin domin dakile yaduwar rikicin da dawo da zaman lafiya.

Sojoji sun farmaki Kachalla Murtala a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai wani farmaki kan 'yan bindiga a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun samu nasarar wargaza maboyar 'dan bindiga Kachalla Murtala.

Sojojin Najeriya sun ceto wata mata da ta shafe sama da wata biyu a hannun 'yan bindiga masu garkuwa a cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng