Wata Sabuwa: Fasto Ya Faɗi Abin da Ya Yi Sanadin Fafaroma Saɓanin Rahotanni
- Fasto Chris Oyakhilome ya ce allurar rigakafin COVID-19 ce ta kashe Fafaroma Francis, yana danganta mutuwarsa da hadin kai da masu mulki
- A cikin wani bidiyo, Oyakhilome ya soki Fafaroma saboda goyon bayan rigakafin, yana cewa lafiyarsa ta tabarbare bayan karɓar allura
- Ya ce shanyewar jiki da ta yi sanadin mutuwar Fafaroma ta samo asali ne daga toshewar jini da allurar rigakafin ke haddasawa da cewa ana boye gaskiya
- Hukumar Vatican ta ce Fafaroma ya mutu sakamakon shanyewar jiki da rashin aikin zuciya, inda suka ce yana da wasu cututtuka na baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fasto Chris Oyakhilome na 'LoveWorld Incorporated' ya yi zargi kan mutuwar Fafaroma Francis.
Faston ya zargi cewa allurar rigakafin COVID-19 ce ta janyo mutuwar Fafaroma Francis.

Asali: Getty Images
Fasto ya yi zargi kan mutuwar Fafaroma Francis
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Oyakhilome ya ce goyon bayan Fafaroma ga rigakafin ya hada shi da masu mulki duniya, cewar Tribune m
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa Fafaroma ya karfafi jama'a su karɓi rigakafin, inda ya zargi wannan shawara da kasancewa kuskure.
Oyakhilome ya ce shanyewar jikin da ta yi sanadin mutuwar Fafaroma Francis ta faru ne sakamakon toshewar jini da allurar rigakafin ta haddasa.
Ya ci gaba da cewa akwai wasu mutuwar da aka boye gaskiyarsu, yana zargin cewa gwamnati da wasu hukumomi sun rufe gaskiyar allurar rigakafin.
Ya ce:
"Fafaroma ya ce idan Yesu yana duniya, zai karbi allura, na ce wannan maganar ba ta dace ba, ta ci mutunci.
"A lokacin yana tare da masu mulki, ya karbi rigakafin, amma tun bayan nan bai sake samun lafiya ba har ya mutu.
"Jiya ko kwana biyu da suka gabata, sun ce ya samu shanyewar jiki. Ina tambaya, daga ina shanyewar ta fito? Toh, toshewar jini ne.

Asali: Facebook
Fasto ya bankaɗo sharrin rigakafin Covid-19
Faston ya ce mutane da dama sun mutu amma ba za a fadawa al'umma gaskiya ba saboda ba za a iya warkar da su ba har su mutu.
Ya kara da cewa:
"Mutane suna mutuwa, amma ba su fada maku gaskiya ba. Sun rikice, ba za a warkar da su ba, har su mutu.
"Sun kira shi 'sudden death syndrome', Ku tuna, na taba fada muku cewa rigakafin nan na kashe mutane ne a ko'ina a duniya.
"Babu wani tsarin kimiyya da zai cire shi daga jiki. An tsara shi ne da gangan domin hallaka mutane da yawa a duniya.
Me zai faru bayan rasuwar Fafaroma?
Kun ji cewa Fafaroma Francis ya rasu yana da shekaru 88 bayan shekara 12 yana jagorantar cocin Katolika, wadda ke da mabiya biliyan 1.4 a duniya.
Rasuwarsa ta janyo an soma bin tsarin zaɓen sabon Fafaroma da aka gada tun kaka da kakanni, wanda manyan jami'ai 138 ke gudanarwa.
Rahoton Legit Hausa ya yi bayanin yadda ake zaben sabon Fafaroma, masu zaben da wanda ya cancanci zama jagoran Katolika.
Asali: Legit.ng