An Shiga Fargaba a kan Makomar Najeriya, An Gano Abin da zai Wargaza Kasa

An Shiga Fargaba a kan Makomar Najeriya, An Gano Abin da zai Wargaza Kasa

  • Tsohon Sakataren Kungiyar kasashen rainon Ingila, Cif Emeka Anyaoku ya yi gargadin cewa Najeriya za ta iya wargajewa
  • A cewar Anyaoku, yankunan Najeriya na da ikon tafiyar da kansu a shekaru shida na farko bayan samun ‘yancin kai, ba kamar yanzu ba
  • Ya ce matukar ana so kasar Najeriya ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya, sai an koma tsarin mulkin tarayya na hakika

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Sakataren Kungiyar kasashe rainon Ingila, Emeka Anyaoku, ya sake yin kira mai karfi ga Najeriya da ta rungumi tsarin mulkin da duk yan kasa za su mora.

Ya yi gargadin cewa kasar na fuskantar barazanar rugujewa matukar aka ci gaba da tafiya a karkashin tsarin mulki da ake kai a halin yanzu.

Tinubu
An shawarci Najeriya kan tabbatar da zaman lafiya a kasa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Anyaoku ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ranar Talata, wanda aka yi yi magana a kan muhimmancin ingantaccen mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin jawabin nasa, Cif Anyaoku ya bayyana cewa tsarin mulkin tarayya ne kadai zai iya ceto Najeriya daga fadawa halin da wasu kasashe masu yawan kabilu da yawa suka fada.

Najeriya ta fi samun ci gaba a baya — Anyaoku

Cif Emeka Anyaoku ya jaddada cewa Najeriya ta fi samun zaman lafiya da ci gaba a cikin shekarun farko na ‘yancinta daga Turawan mulkin mallaka,.

Ya ce an ga ci gaba sosai a cikin shekaru shida na farko bayan samun ‘yanci, domin a wancan lokacin, kasar tana amfani da sahihin tsarin mulkin tarayya.

Tinubu
Shugaban Najeriya na yanzu, Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce:

“Kowanne daga cikin yankuna hudu da ake da su a lokacin na da cikakken iko kan ci gaban yankinsu, harkokin jin dadin jama’a da kuma tsaron cikin gida.”

An shiga fargaba kan makomar Najeriya

A jawabinsa yayin taron, tsohon Ministan harkokin waje kuma tsohon babban jami’in soji, Manjo Janar Ike Nwachukwu (mai ritaya), ya goyi bayan matsayar Anyaoku.

Janar Ike Nwachukwu (mai ritaya) ya kara da bayyana cewa tsarin mulkin Najeriya na yanzu ya gaza kuma yana bukatar gyara idan ana son ci gaba da wanzuwar zaman lafiya.

Ya ce:

“Saboda wannan dalili ne tun da dadewa nake fafutikar a sake fasalin Najeriya zuwa cikakken tsarin tarayya."
"‘Yancin jihohi yana da matukar muhimmanci – yana kusantar da mulki zuwa ga talakawa kuma yana basu damar amfani da albarkatun yankunansu don ci gaba.”

An gano dalilin faduwar Atiku a zaben Najeriya

A wani labarin, mun wallafa cewa Sanata mai wakiltar mazabar Benue ta Kudu, Abba Moro, ya bayyana cewa saura kiris jam’iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Sanata Moro ya bayyana cewa babban kuskure ne jam’iyyar PDP ta yi shi ne tsaida tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakin Atiku Abubakar a zaben da ya gabata.

Sanatan ya bayyana hakan ne sa’o’i bayan da Okowa kansa ya fito fili ya bayyana nadamarsa na yin tafiya da Atiku Abubakar a zaben 2023, amma Moro ya zarge shi da gaza taimakon PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.