Matakin da Yan Sanda Suka Dauka kan Farmakin Tawagar Pantami a Gombe

Matakin da Yan Sanda Suka Dauka kan Farmakin Tawagar Pantami a Gombe

  • Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta fara bincike kan harin da wasu da ake zargin 'yan bangar siyasa ne suka kai a jihar
  • Maharan sun kona tayoyin mota tare da fasa gilashin wasu motoci a yankin Jekadafari yayin da Isa Pantami ya isa Gombe
  • 'Yan sanda sun ce ba a kama wani mutum ba tukuna, amma za su gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe – Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta fara bincike kan harin da wasu da ake zargin 'yan bangar siyasa ne suka kai wa ayarin motocin Farfesa Isa Ali Pantami.

Harin ya faru ne a yankin Jekadafari lokacin da dan takarar PDP ya isa jihar Gombe ta jirgin haya, inda daruruwan magoya bayansa suka tarbe shi.

Kara karanta wannan

An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

Yan sanda sun fara bincike kan farmakin Pantami
Kakakin yan sanda a Gombe, Buhari Abdullahi Dan Romi.
Source: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ya tabbatar wa jaridar Arewa Punch faruwar lamarin a ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin maharan sun kunna wuta da tayoyin mota tare da fasa gilashin motocin da ke cikin ayarin.

Magoya bayan Isa Ali Pantami sun taru ne a fadar mai martaba Sarkin Gombe domin halartar taron gabatar da tutocin jam'iyyu ga 'yan takarar da za su fafata a zaɓen 2027.

'Yan sanda sun fara binciken harin Pantami

Kakakin rundunar ya bayyana cewa kawo yanzu ba a kama wani mutum da ake zargi da hannu a harin ba, amma jami'an tsaro sun fara bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.

A cewarsa, an tura isassun jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, amma wasu bata-gari sun yi amfani da cunkoson jama'a wajen kai hare-hare kan motocin da suka rage a bayan jerin gwanon.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

"Har yanzu ba mu kama kowa ba, amma muna gudanar da bincike. Kamar yadda kuka gani, an tura jami'an tsaro yadda ya kamata. Sai dai lokacin da taron jama'a ya wuce wani wuri, wasu 'yan bangar siyasa suka fara tare motocin da suka rage tare da kai musu hari."
An kai farmaki kan tawagar Pantami
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Dangane da adadin motocin da harin ya shafa, kakakin 'yan sandan ya ce ba su iya tantance adadin ba saboda babu wanda ya kai ƙorafi a hukumance zuwa ofishin 'yan sanda.

Ya ƙara da cewa abin da suke da shi a yanzu shi ne bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ba zai wadatar wajen tabbatar da adadin motocin da aka lalata ba.

'Yan sanda sun yi barazanar hukunta maharan

Buhari Abdullahi ya tabbatar wa al'ummar jihar cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da bincike da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a harin.

Ya kuma yi gargaɗi ga 'yan siyasa da magoya bayansu kan kauce wa duk wani nau'in tashin hankali yayin gudanar da harkokin siyasa.

Kakakin ya tuna cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya sha yin gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci daba ko tashin hankali na siyasa ba.

Kara karanta wannan

Amnesty ta bukaci a kama 'yan daban da suka kai wa Pantami hari a Gombe

Pantami ya magana kan mulkin Gombe

A wani labarin, an ji cewa Farfesa Isa Pantami ya soki abokan hamayyarsa, yana mai cewa idan aka zaɓe shi gwamna, zai kare dukiyar al'ummar jihar maimakon raba ta.

Pantami ya ce wasu 'yan siyasa na iƙirarin cewa za su raba kuɗaɗen jihar idan suka samu mulki, amma shi zai mayar da hankali wajen kare dukiyar jama'a.

Tsohon ministan ya kuma yi tsokaci kan yadda aka naɗa shi a wani muƙamin gwamnati, inda ya kwatanta kansa da wasu 'yan siyasa daga Wurono da ke jihar Jigawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.