Ana Wata ga Wata: Sabuwar Barazana Ta Tunkaro Sanata Natasha kan Zamanta a Majalisa

Ana Wata ga Wata: Sabuwar Barazana Ta Tunkaro Sanata Natasha kan Zamanta a Majalisa

  • Mutanen mazaɓar sanatan Kogi ta Tsakiya sun gaji da salon wakilcin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Wasu daga cikin mazauna yankin sun fara shirin yi mata kiranye daga majalisar dattawa saboda abin da suka kira rashin iya wakilci
  • Sai dai, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta ce ba ta da masaniya kan shirin yi wa Sanata Natasha kiranye

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Wasu mazauna mazaɓar Sanatan Kogi Tsakiya sun fara aiwatar da shirin tunɓuke Natasha Akpoti-Uduaghan daga kujerarta.

Mutanen sun fara shirin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye ne saboda rashin gamsuwa da wakilcinta.

Za a yi wa Sanata Natasha kiranye
An fara yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce an fara yunƙurin a ƙaramar hukumar Okehi a ranar Laraba, inda ɗimbin masu zaɓe suka fito don nuna goyon bayansu ga shirin tunɓuke sanatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake son yi wa Natasha kiranye?

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnatin Tinubu ta fadi gatan da za ta yi wa 'shugaban rikon kwarya'

Daya daga cikin masu zaɓe, Nura Ibrahim, ya bayyana cewa wannan aiki yana gudana ba tare da la’akari da jam’iyya ba.

Ya ce al'ummar yankin na yawan rashin jin daɗin wakilcin Sanata Natasha, musamman wajen warware matsalolin talauci, ababen more rayuwa da ilimi.

“Ba a yanke shawarar fara wannan yunƙuri da wasa ba, domin manyan masu ruwa da tsaki sun sha ƙoƙarin tattaunawa da ita a lokuta da dama, amma ƙoƙarinsu ya ci tura sakamakon girman kai da raini daga gare ta."

- Nura Ibrahim

Ana sa ran wannan shirin zai ɗauki kwanaki biyu a dukkan rumfunan zaɓe dake cikin ƙananan hukumomi biyar na Kogi ta Tsakiya.

A cikin wannan lokaci, za a buƙaci al’ummar yankin su sa hannu a wata takarda da ke buƙatar tunɓuke sanatar daga mukaminta.

Sai dai wasu rahotanni sun ce wasu mazauna yankin an yaudare su ne wajen sanya hannu, bayan da wani mai shela ya zagaya Okehi a ranar Talata yana gayyatar jama’a domin wani shirin tallafi.

Kara karanta wannan

Ba jira: Ministan Tsaro, Matawalle ya fadi shirin sojoji kan dokar ta baci a Rivers

Amma da suka isa wurin, sai aka buƙaci su bayar da lambar katin zaɓe domin a ba su kuɗi, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Me hukumar INEC ta ce kan lamarin?

Kwamishinan INEC na jihar Kogi, Gabriel Longpet, ya bayyana cewa bai da masaniya kan shirin yi wa sanatar kiranye.

“Ba ni da masaniya kan wani yunƙurin yi wa Sanata Natasha kiranye, sai dai rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta."
“Babu wanda ya tuntube ni kan wani kiranye daga kowane yanki na jihar Kogi."

- Gabriel Longpet

Natasha ta sake sabon zargi kan Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta haƙiƙance kan zargin da take yi wa Godswill Akpabio.

Sanata Natasha ta yi zargin cewa har a cikin zauren majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya taɓa nuna mata alamar yana son ya yi lalata da ita.

Kara karanta wannan

Rivers: Abin da manyan lauyoyi ke cewa kan matakin Tinubu na sa dokar ta baci

Natasha ta kuma yi zargin cewa majalisar dattawa na azabtar da ita tare da ƙoƙarin toshe mata baki saboda zargin da take yi kan Akpabio.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng