El Rufa'i Ya Dauko Ruwan Dafa Kansa bayan Kiran 'Yan Majalisar Kaduna 'Jalilai'
- 'Yan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna sun yi barazanar daukar matakin shari'a kan tsohon gwamna watau Nasir El-Rufa'i
- 'Yan majalisar sun fusata ne da tsohon gwamnan ya kira su da jahilai, marasa ilimi da nagartar da za su binciki gwamnatinsa
- Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Henry Marah Zachariah ya ce ba za su zauna El-Rufa'i ya na ci masu mutunci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - 'Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun yi barazanar daukar matakin shari’a kan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i.
‘Yan majalisar sun fusata bayan da aka ruwaito cewa El-Rufa'i ya kira su "jahilai marasa ilimi" a wata hira da ya yi da manema labarai a jihar.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa, Hon. Henry Marah Zachariah, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, ya bayyana cewa ‘yan majalisar ba za su lamunci irin wannan cin mutunci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ‘yan majalisar suna da cancantar shari’a, ilimi da kuma nagarta, kuma sun yi aiki tukuru wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu na bincikar tsohon gwamnan.
Kalaman El-Rufa’i da suka fusata ‘yan majalisa
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa a yayin wata hira da ya yi a wani gidan rediyo, El-Rufa’i ya kira ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna da “jahilai marasa ilimi”.
Ya kara da cewa ‘yan majalisar ba su da ilmin da ake bukata da zai ba su damar gudanar da bincike a kan gwamnatinsa ko da ya yi ba daidai ba a ofis.

Asali: Facebook
Da yake mayar da martani, Hon. Zachariah ya ce:
“Muna so mu tunatar da tsohon gwamna cewa dukkan 'yan wannan majalisa ta cika sharuddan da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada a sashe na 106 domin su tsaya takara kuma su ka ci zabe.”
"'Yan majalisar suna da cancantar shari’a, ilimi da kuma nagarta, kuma sun yi aiki tukuru wajen cika hakkin da kundin tsarin mulki ya dora musu na bincike.”
Majalisa ta magantu kan binciken El-Rufa’i
Hon. Zachariah ya bayyana cewa sakamakon binciken da kwamitin majalisar ya gudanar kan tsohon gwamnan da gwamnatinsa na nan a fili.
Ya kara da cewa duk wani yunkuri da El-Rufa’i ya yi na kalubalantar rahoton a kotu bai yi nasara ba, kuma tsohon gwamnan zai zama wanda ake tuhuma har sai kotu ta wanke shi.
El-Rufa’i: Majalisar Kaduna za ta garzaya kotu
‘Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun ce za su dauki matakin shari’a kan El-Rufa’i bisa cin mutuncinsu ta hanyar kiran su "jahilai marasa ilimi”.
Sun ce:
“Dangane da batun cin mutuncin 'yan majalisa, inda aka ce jahilai ne marasa ilimi, majalisar za ta dauki matakin shari’a da ya dace domin kare mutuncinta."
Hon. Zachariah ya jaddada cikakken goyon bayan ‘yan majalisar ga Gwamna Uba Sani da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Yusuf Liman.
Ciyamomin jihar Kaduna sun soki El-Rufa'i
A baya, mun wallafa cewa kungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON), reshen jihar Kaduna, ta yi martani mai zafi kan zargin da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i.
Tsohon gwamnan ya zargi gwamna Uba Sani da karkatar da kudin kananan hukumomi, lamarin da ALGON ta bayyana a matsayin labarin karya mara tushe ko makama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng