Ana Tsakiyar Farautar Bello Turji, Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Hafsoshin Tsaro

Ana Tsakiyar Farautar Bello Turji, Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Hafsoshin Tsaro

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Aso Villa, inda manyan jami’an tsaro suka halarci taron a ranar Talata
  • Babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu; da daraktan DSS sun halarci zaman
  • Ba a san dalilin taron ba, amma ana hasashen yana da alaƙa da matsalar tsaro,, musamman rikice-rikicen da suka addabi wasu yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro na Najeriya a ranar Talata, a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; da daraktan hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi, sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Fubara, Shugaba Tinubu ya naɗa 'gwamnan riko' a jihar Ribas

Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya
Tinubu ya kira taron manyan hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban kasa. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro a Villa

Channels TV ya rahoto cewa Tinubu ya saka labule da shugabannin tsaron ne karkashin jagorancin shugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio; da jagoran masu rinjaye, Opeyemi Bamidele, daga baya suka shiga taron da aka gudanar a ofishin shugaban ƙasar.

Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da mataimakinsa, Ben Kalu, suma an hange su a wurin taron.

Ana hasashen dalilin kiran wannan taro

Ba a bayyana ajandar taron ba a lokacin da aka fitar da wannan rahoto, amma ana kyautata zaton yana da alaƙa da matsalar tsaro da ta shafi ƙasar nan.

Daily Trust ta tattaro cewa ana sa ran shugabannin tsaro za su gabatar wa Shugaba Tinubu bayani kan halin tsaro a ƙasar tare da tsara matakan magance matsalolin da ke akwai.

Ana kuma hasashen cewa taron na iya kasancewa ɗaya daga cikin zaman tattaunawar tsaro na yau da kullum, inda shugaban ƙasa ke karɓar rahoto daga shugabannin tsaronsa.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, ya nada sabon shugaba

Me ya biyo bayan taron hafsoshin tsaro?

Tinubu ya dakatar da gwamnatin Fubara, ya ayyana dokar ta baci a Ribas
Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Ribas, ya dakatar da Gwamna Fubara. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Awanni da kammala taron, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers, yana mai kafa hujja da rikicin siyasa da kuma nakasun gudanar da mulki.

Shugaban ƙasar ya kuma dakatar da Gwamna Sim Fubara, mataimakinsa da mambobin majalisar dokokin jihar har na tsawon watanni shida, in ji Vanguard.

A wata sanarwa ta gaggawa da ya yi a faɗin ƙasa a ranar Talata, Tinubu ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a jihar.

Shugaban kasar ya na naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin 'gwamnan riko' jihar domin amfanin al’ummar Rivers.

Ayyanar da dokar ta-ɓacin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan wani fashewar tanka da aka samu a wata cibiyar mai da ke ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni.

Tsige Fubara: Bututun mai ya fashe a Ribas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu fashewar bam a bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP) da ke Bodo, a karamar hukumar Gokana ta jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Wike ya soke takardun filaye kusan 5000, an fadi sharadin mayar wa jama'a dukiyarsu

Rahotanni sun bayyana cewa wata gobara ta tashi a yankin bayan fashewar bam din, inda ake ganin bakin hayaki na tashi sama.

Duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da musabbabin fashewar ba tukuna, ana zargin cewa 'yan bindiga da suka yi barazanar kai hari ne ke da hannu a lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.