Shugaban APC Ya Fede Gaskiya kan Takaddamar Akpabio da Sanata Natasha

Shugaban APC Ya Fede Gaskiya kan Takaddamar Akpabio da Sanata Natasha

  • Shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa ya bayyana ra'ayinsa kan dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Aliyu Bello ya bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ta yi daidai da dokokin da ake amfani da su a majalisar dattawa
  • Alhaji Bello bayyana cewa bai kamata a riƙa kallon dakatarwar a matsayin cewa Godswill Akpabio na ƙoƙarin nuna mata wariya ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, Aliyu Bello, ya yi magana kan taƙaddamar Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Shugaban na APC ya bayyana cewa matakin da majalisar dattawa ta ɗauka na dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida ya dace.

Shugaban APC ya goyi bayan dakatar da Sanata Natasha
Shugaban APC na Nasarawa ya goyi bayan dakatar da Sanata Natasha Hoto: Nigerian Senate, Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Aliyu Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana ra'ayinsa kan dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha, sun yi mata babban alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta shigar da ƙorafi tana zargin cewa shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ci zarafinta.

Me shugaban APC ya ce kan dakatar da Natasha?

Aliyu Bello ya ce dokokin majalisar dattawa suna buƙatar a hukunta duk wani ɗan majalisa da ya aikata abin da aka ɗauka a matsayin karya doka ko raina majalisa.

"Dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya jawo cece-kuce, inda wasu ke zargin cewa an yi mata hakan ne saboda ita mace ce, kuma shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio na nuna wariya."
"Duk da cewa batun rashin daidaito tsakanin maza da mata a siyasa yana buƙatar taka tsan-tsan, cakuɗa hukuncin majalisa na yau da kullum da zargin wariya ga mata na iya rage muhimmancin ƙoƙarin da ake yi na samun daidaito a siyasa."
"Idan aka duba abin da ya faru a baya da kuma yadda ake gudanar da al’amuran majalisa, za a fahimci cewa dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bai saɓawa tsarin majalisa ba, domin ana yin hakan ga kowane ɗan majalisa ba tare da la’akari da jinsinsa ba."

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

"Majalisar Dattawa tana da tarihin dakatar da mambobinta maza da mata idan sun karya dokokinta. A shekarar 2018, an dakatar da Sanata Ovie Omo-Agege na tsawon kwanaki 90 bayan ya soki gyaran dokar zaɓe."
"Haka nan, a shekarar 2012, an dakatar da Sanata Abdul Ningi bayan ya zargi tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da karɓar Naira miliyan 500 a kowane wata."
"A shekarar 2023, an dakatar da Sanata Abdul Ahmed Ningi na tsawon watanni uku kan zargin cushe a kasafin kuɗi."
"Duk a waɗannan lokutan hukuncin ya shafi maza ne, amma ba a taɓa danganta su da nuna wariya ba. To, me ya sa ake ɗaukar hukuncin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da wata fuska daban?"
"Dokokin majalisar dattawa sun tanadi hukunci ga duk wanda ya aikata wani abu da aka ɗauka a matsayin cin zarafi ko raina majalisa."
"Darajar wannan cibiya ta dogara ne kan aiwatar da waɗannan dokoki ba tare da nuna bambanci ba."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki kan zargin shugaban Majalisa da neman matar aure

"Duk wani zargin cewa Sanata Akpabio ya ɗauki matakin ne kawai don ya hukunta wata mace ba ya da tushe, kuma ya kaucewa gaskiya da tsarin doka."

- Aliyu Bello

Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin sanatocin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya sun kai kai ziyara ga Sanata Natasha Akpoti Uduaghan.

Sanatocin waɗanda suka ziyarce ta bayan dakatarwar da aka yi mata a majalisa, sun bayyana cewa za su goya mata baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng