Badaƙalar $300m: Majalisa Ta Ba Ministan Tinubu Sa’o’i 72 Ya Gurfana Gabanta, Sun Samu Bayanai

Badaƙalar $300m: Majalisa Ta Ba Ministan Tinubu Sa’o’i 72 Ya Gurfana Gabanta, Sun Samu Bayanai

  • Majalisar wakilai ta tarayya za ta binciki ma'aikatar lafiya kan yadda ta kashe $300m da aka ware domin yaki da zazzabin cizon sauro
  • Majalisar ta kuma ba ministan lafiya da babbar sakatariyar ma'aikatar wa'adin sa'o'i 72 su bayyana a gabanta ko su fuskanci fushinta
  • Akwai zarge-zarge da ake yi wa ma'aikatar lafiyar na karkatar da kudi da kuma hana kamfanonin gida sayo gidajen sauro da magunguna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta tarayya ta nemi ministan kiwon lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate da ya gurfana gabanta domin amsa tambayoyi kan kudaden da aka kashe a yaƙi da zazzabin cizon sauro.

Majalisar na zargin cewa ma'aikatar lafiya ta karkatar da $300m da aka ware domin daƙile cutar zazzaɓin cizon sauro a 2021.

Kara karanta wannan

Abin da majalisar dattawa ta buƙaci Tinubu ya yi wa iyalan sojojin da aka kashe a Delta

Majalisar wakilai za ta gana da ministan lafiya, Ali Pate
Badaƙalar $300m: Majalisa ta nemi ganawa da ministan Tinubu. Hoto: @muhammadpate, @HouseNGR
Asali: Facebook

Haka zalika, kwamitin majalisar kan yaki da zazzabin cizon sauro, kanjamau da tarin fuka, ya nemi ganawa da babbar sakatariyar ma'aikatar lafiyar domin ba da ba'asin yadda aka kashe kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista, Kachollom na fuskantar kamun majalisa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kwamitin, Amobi Godwin Oga, ya bayar da umarnin gayyatar bayan matsayar da kwamitin ya cimmawa a ranar Talata.

Haka kuma, za a binciki ministan da babbar sakatariyar ma'aikatar, Daju Kachollom, kan zargin sun hana wasu kamfanoni kwangilar samar da gidajen sauro da magangunguna.

A cewar shugaban kwamitin, babbar sakatariyar ma'aikatar na iya fuskantar kamu sakamakon gaza amsa gayyatar kwamitin har sau uku.

Ma'aikatar lafiya ta ƙi ba da haɗin kai?

Kwamitin ya bankado cewa ma'aikatar lafiya ta fitar da $3m da zimmar sayen gidan sauro da sauran kayayyakin yaki da cutar.

Kara karanta wannan

Abdul Ningi: Akwai yiwuwar sanata zai koma kujerarsa amma da sharadi, Akpabio na cikin matsi

Oga ya ce:

"Abin da muke so mu sani shi ne, sun yi amfani da kudin? Idan ba su yi amfani da kudin ba to ina suka maƙale? Amma sai wani zulle-zulle suke yi.
"Ba za muyi ƙasa a guiwa ba wajen amfani da karfin ikon majalisa na sa wa a kama babbar sakatariyar ma'aikatar, domin abin na nema ya wuce gona da iri."

Majalisa ta ba minista wa'adin sa'o'i 72

Rahoton Premium Times ya nuna cewa majalisar ta karbi wani korafi a makonnin da suka gabata, daga wani kamfani, Rosies Textile Mills Limited.

Kamfanin ya shigar da koke kan cewar ma'aikatar lafiya ta hana kamfanonin gida damar samun kwangilar sayo gidajen sauro da magungunan yaki da zazzabin sauron.

Da wannan ne majalisar ta ba ministan da babbar sakatariyar ma'aikatar lafiya awanni 72 su bayyana a gaban kwamitin.

Zargi: Ministan Tinubu ya aika laifuffuka 3?

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa, akwai wasu manyan badakaloli uku da ake zargin ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ola ya aikata.

Duk da cewa ana kallon Tunji-Ola a matsayin tauraro a gwamnatin Tinubu, sai dai ya fuskanci zarge-zarge da suka so bata masa suna tun a lokacin da ya ke ɗan majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel