Ana Murnar Fara Azumi, Sanatan Arewa Ya Shirya Gagarumin Bikin Tallafawa Talakawa
- Sanata Saliu Mustapha ya horar da mutane fiye da 2,500 a Kwara kan harkar noma, kasuwanci da sana’o’i, tare da raba masu kayan aiki
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da ministan noma, Abubakar Kyari, sun halarci taron domin karfafa Sanata Saliu
- An gudanar da taron a Ilorin, inda Sanata Jibrin da takwarorinsa suka bayar da injunan dinki 200 don tallafawa al’ummar Kwara ta Tsakiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Sanata Saliu Mustapha ya bai wa mutane fiye da 2,500 tallafi domin bunkasa harkokin kasuwanci, noma, da sana’o’in hannu a jihar Kwara.
Wannan tallafin na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi a Najeriya da kasashen duniya ke murnar fara azumin watan Ramadan na 2025.

Asali: Twitter
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da ministannoma, Abubakar Kyari, sun yabawa Sanata Saliu da kawo wannan shiri, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban Majalisa ya goyi bayan kudirin ƙirkiro jiha 1 a Arewa, an faɗi sunanta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan Kwara ya tallafawa 'yan mazabarsa
Sanata Barau da Abubakar Kyari sun ce wannan shirin na Sanata Saliu ya yi daidaita da manufofin Shugaba Bola Tinubu na inganta rayuwar al'umma.
Sanata Saliu, mai wakiltar Kwara ta Tsakiya (APC), ya raba kayan tallafi ga mata, manoma, da masu sana’o’i a birnin Ilorin na jihar Kwara.
Ya ce shirin zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu cin gajiyar shirin sun dogaro da kansu ta hanyar basu kayan aiki da horo na musamman.
"Shirin da aka gabatar na yau ya nuna manufarmu ta tallafawa dukkanin wadanda muka horar da su. Mun yanke shawarar horar da su a matakai daban daban.
“Mun horar da su kan yadda ake hadawa, gyarawa da kula da na'urorin ba da wuta da hasken rana, kuma za su sami kayayyakin aiki yau."
- Inji Sanata Mustapha.
Barau ya yi magana a taron ba da tallafin

Kara karanta wannan
Ramadan: Ɗan majalisa a Arewa ya tara talakawa, ya raba masu kudi da kayan abinci
An gudanar da shirin mai taken: 'Alubarika 1.0: Shirin bunkasa mutane kan noma da gina rayuwa' a birnin Ilorin, a ranar Juma’a.

Asali: Twitter
Sanata Jibrin da sauran ‘yan majalisa sun bayar da gudunmawar injunan dinki 200 ga al’ummar Kwara ta Tsakiya..
Mataimakin shugaban majalisar ya ce:
“Mun hallara a nan a yau domin karfafawa Sanata Mustapha saboda kokarinsa wajen bunkasa noma da ci gaban al'ummar mazabarsa.”
Sanata Jibrin ya jaddada cewa noma na da matukar muhimmanci, domin babu wata al’umma da za ta cigaba ba tare da abinci ba.
Ya kara da cewa shirin da Sanata Saliu ya gudanar ya dace da kudirin Shugaba Tinubu na samar da abinci ga kowa a Najeriya.
Ministan noma ya jinjinawa kokarin Sanata Saliu
Ministan noma, Abubakar Kyari, ya yabawa Sanata Mustapha bisa jajircewarsa wajen aiwatar da ayyukan da ke inganta samar da abinci a kasa.
Kyari ya ce irin wadannan shirye-shirye na tallafawa gwamnati wajen tabbatar da wadatar abinci da rage fatara a Najeriya.
Masu cin gajiyar shirin sun nuna godiyarsu, suna masu cewa hakan zai bunkasa harkokinsu na kasuwanci, noma da kuma rayuwarsu ta yau da kullum.
Duba hotunan taron da sanatan ya dora a shafinsa na X.
Dan majalisa ya rabawa talakawa 5000 tallafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan majalisar Kaga/Magumeri/Gubio a jihar Borno, Hon. Usman Zannah, ya tallafawa al’ummarsa yayin da aka fara azumin Ramadan.
Kayayyakin tallafin da dan majalisar ya raba sun haɗa da shinkafa, sukari, taliya da kudi, wanda ya ce ya saba rabawa domin al'umma su yi azumi cikin walwala.
Asali: Legit.ng