'Ba Ka Isa ba': Lauya Ya Nuna Gwamna da Yatsa kan Hana Haƙar Ma'adanai a Arewa
- Barista Ayodele Kusamotu ya ce Gwamna Caleb Mutfwang ya sabawa kundin tsarin mulki da ya hana hana hakar ma’adinai a jihar Filato
- Lauyan ya ce hakar ma’adinai na karkashin ikon gwamnatin tarayya ne kadai, kuma dakatar da shi zai hana masu zuba jari shigowa Filato
- Kusamotu ya bukaci gwamnan da ya maida hankali kan matsalar tsaro, yana mai sukar yadda kotuna ke hana hakar ma’adinai haka kurum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Wani lauya, Ayodele Kusamotu ya ce Gwamna Caleb Mutfwang ba shi da ikon dakatar da hakar ma’adinai a Filato ta hanyar dokar zartarwa ta 001.
A ranar 21 ga Fabrairu, Gwamna Mutfwang ya sanar da dakatar da ayyukan hakar ma’adanai a fadin jihar bisa dalilan tsaro, yana mai cewa dakatarwar ta fara aiki nan take.

Asali: Twitter
Lauya ya kalubalanci gwamnan jihar Filato
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Kusamotu ya bayyana dokar zartarwar a matsayin wanda ta sabawa kundin tsarin mulkin kasa, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dokar 1999 ta Najeriya ta sanya hakar ma’adanai a jerin dokokin da ke karkashin ikon gwamnatin tarayya kadai, don haka ba ikon gwamna ba ne dakatar da ayyukan ma’adanai.
Lauyan ya ce dokar da Gwamna Mutfwang ya zartar ba ta da inganci kuma tana da illa ga ci gaban tattalin arzikin jihar Filato da kasa baki daya.
“Wannan matakin zai sa masu zuba jari su guji jihar Filato, har ma da Najeriya gaba daya,” in ji Kusamotu.
'Ka shawo kan matsalar tsaro' - Lauya ga gwamna
Lauyan ya kara da cewa ambaton batun tsaro ba dalili ba ne na hana hakar ma’adanai, yana mai kwatanta matakin da hana mutane fita waje saboda barazanar ‘yan bindiga.
Kusamotu ya bukaci gwamnan ya maida hankali kan shawo kan matsalolin tsaro maimakon kutsawa cikin hurumin ma’aikatar ma’adanai ta tarayya.
Ya ce kotunan yankin a jihar Filato na yawan bayar da umarni na hana ayyukan hakar ma’adanai, yana mai cewa hakan na haifar da matsala ga masu hakar ma’adanai da ke da lasisi.

Asali: Twitter
Lauyan ya yi zargin cewa ana kokarin yaudarar jama’a da labaran da ba su dace ba domin nuna cewa ana daukar mataki kan hakar ma’adanai.
Halin da masu hakar ma'adanai ke ciki
Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kungiyar masu hakar ma'aikata ta Najeriya (MAN) ke tafiyar da al’amura, yana mai cewa zai kafa wata sabuwar kungiya don kare hakkin masu hakar ma’adanai.
Lauyan ya bayyana cewa har yanzu akwai matsaloli da dama da ba a warware ba, ciki har da karin kudaden sabis na shekara-shekara da ministan ma’adanai ya yi ba bisa ka’ida ba.
Kusamotu ya ce masu hakar ma’adanai na fuskantar matsin lamba, amma da dama ba su da kwarin gwiwar kalubalantar wasu matakan da ya ce ba su dace ba, saboda tsoron azabtarwa.
Ya bukaci masu hakar ma’adanai da su fuskanci matsalolin da ke addabar su maimakon yin shiru.
An dage haramcin hakar ma'adanai a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumin da ta sanya kan haƙar ma'adanai a Zamfara tun 2019, wanda zai farfaɗo da masana'antar.
Ministan ma'adanai, Dele Alake, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan inganta yanayin tsaro a jihar da ke fama da ‘yan bindiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng