Filato: An shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka farmaki jama'a, suka kashe da dama

Filato: An shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka farmaki jama'a, suka kashe da dama

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Filato sun tabbatar da kashe wasu mutane a wurin hakar ma'adinai a wani yankin jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta shaida cewa an kashe mutane hudu da basu ji ba basu gani ba
  • Wasu 'yan bindiga ne suka aikata barnar, lamarin da ya haifar da firgici a yankin tsakanin mazauna, inji wata sanarwa

Jihar Filato - Mazauna kauyen Dung da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato sun shiga jimami bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani wurin da ake hakar ma’adinai, inda suka kashe mutane hudu, Channels Tv ta ruwaito.

‘Yan bindigar sun kai farmaki wurin hakar ma’adinan ne a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka harbe ma’aikatan har lahira, lamarin da ya tilastawa rundunar ‘yan sandan jihar ta tura karin jami’anta zuwa yankin.

Kara karanta wannan

Sabon harin ta'addanci: 'Yan bindiga sun afkawa sansanin sojoji a Katsina, sun yi barna

Barnar 'yan bindiga a Filato
Filato: An shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka farmaki jama'a, suka hallaka mutane
Asali: Facebook

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Gabriel Ubah ya fitar ranar Lahadi, ya ce an tura dakarun ne domin dakile tabarbarewar doka da oda.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike da nufin kamo 'yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lokacin da aka tambayi jami'in ko hukumomin 'yan sanda na sane da harin, ya ce:

"Eh, rundunar tana sane da abin da ya faru a Dung.
“Nan take ‘yan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru. Sai dai abin takaicin shi ne, wasu ‘yan bindiga da ba a san su ba sun kashe mutane hudu da suka je wurin hakar ma’adanai. An tsaurara matakan tsaro a yankin.
"A halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano lamuran da suka shafi mutuwarsu da kuma kama wadanda suka aikata wannan mugun aikin."

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

A halin da ake ciki, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Bassa a majalisar wakilai ta kasa, Dachung Musa Bagos, ya yi Allah wadai da lamarin.

Dan majalisar a wata sanarwa da kakakinsa Danja Dafwam Yaks ya fitar a ranar Lahadi, ya ce:

“Na fusata da kuma hasala da kashe-kashen da ake yi a mazaba ta da kewayenta. Ina so in bayyana cewa zan ci gaba da magana kan wadannan munanan dabi’u na mashahuran 'yan ta'adda a cikinmu har sai an kawar da su duka."

Haka kuma ya roki gwamnatin tarayya da na jihohi da su umarci jami’an tsaro da su tunkari matsalar rashin tsaro a fadin jihar da kasa baki daya.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa jaridar Tribune cewa, harin na iya zama na daukar fansa daga Fulani, kasancewar an tsinci gawar wani yaro Bafulatani a yankin.

Sojoji sun kashe hatsabiban masu garkuwa da mutane a Plateau, sun kwato makamai

Kara karanta wannan

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

A wani labarin, rundunar OPSH yayin kokarin ganin ta samar da zaman lafiya a jihar, wasu yankunan Jihar Kaduna da Jihar Bauchi ta samu nasarar halaka wasu masu garkuwa da mutane 3 a Jihar Plateau inda ta kwace makamai a hannun su, The Guardian ta ruwaito.

Kakakin rundunar OPSH, Manjo Ishaku Takwa a wata takarda da ya saki jiya ya ce jami’an rundunar sun samu nasarar ragargazar wadanda ake zargin suna cikin ‘yan gidan yarin da suka tsero a ranar 28 ga watan Nuwamban 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel