Sojoji Sun Firgita 'Yan Fashi da Makami da Suka Tare Hanyoyi a Jihar Kaduna

Sojoji Sun Firgita 'Yan Fashi da Makami da Suka Tare Hanyoyi a Jihar Kaduna

  • Sojojin Najeriya karkashin Operation Safe Haven sun dakile yunkurin fashi da makami a karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna
  • A farmakin da sojojin da suka kai, an ceci mutane biyu da ‘yan fashi suka kai wa hari a wurare daban-daban a ranar 11 ga Fabrairu, 2025
  • Rahotanni sun nuna cewa rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan lamarin domin gano 'yan fashin da suka kai farmaki ga mutanen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Sojojin Najeriya karkashin Operation Safe Heaven sun dakile wani yunkurin fashi da makami tare da ceto wasu mutane biyu a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kai dauki ga mutanen da ‘yan fashi suka tare a kan hanya a wurare daban-daban a daren ranar 11 ga Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Sojoji
Sojoji sun fatattaki 'yan fashi a Kaduna. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa yadda sojojin suka fatattaki 'yan fashin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata sanarwa daga rundunar sojin, an sanar da rundunar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kan lamarin.

Sojoji sun dakile fashi a jihar Kaduna

A cewar rundunar soji, harin farko ya faru ne da misalin karfe 7:45 na dare a kan hanyar Wasa–Ankwa.

Sojojin sun samu kiran gaggawa daga mutanen gari, inda suka gaggauta isa wurin don tunkarar ‘yan fashi da makami da suka tare hanyar.

Lokacin da barayin suka hangi sojojin suna isowa, sai suka tsere zuwa daji tare da barin wanda suka tare, mai suna Benjamin Yakubu.

Sojojin sun bude hanyar tare da dawo da harkokin zirga-zirga a wurin, sannan suka kai Benjamin Yakubu asibitin Gwantu don samun kulawa.

Sojoji sun fatattaki 'yan fashi da makami

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

Bayan sa’a guda da ceton Benjamin Yakubu, 'yan fashi sun sake kokarin kai hari a kan hanyar Unguwan Mallam–Aboro da misalin karfe 8:45 na dare.

Wani mutum mai suna Malam Bashir Ibrahim na kan hanyarsa ta komawa gida ne ‘yan bindiga suka tare shi.

Sojojin da ke sintiri a yankin Unguwan Mallam sun samu labari, inda suka garzaya wurin domin cetonsa.

Bayan isowarsu, maharan suka tsere ba tare da cin ma manufarsu ba, inda aka ceto Malam Ibrahim tare da kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.

'Yan sanda sun fara bincike kan harin

A yayin da ake ci gaba da shirin tabbatar da tsaro a yankin, dakarun soji sun sanar da ‘yan sanda domin gudanar da bincike kan lamarin.

Binciken zai taimaka wajen gano wadanda suka aikata harin da kuma daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

An kama mai safarar makamai yana shirin mika bindigogi ga 'yan ta'adda

Rundunar sojin Operation Safe Haven ta tabbatar da aniyar ta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kokarin hana aikata laifuka a yankin Sanga da sauran wurare.

Sojoji sun harbe dan bindiga a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun harbe wani kangararren dan bindiga a jihar Filato.

Dan bindigar ya fara kokuwa da wani soja a cikin daji a lokacin da ya jagoranci sojoji da nufin cewa zai nuna musu wajen da yake boye makamai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng