'Qur'anic Convention': Sheikh Bala Lau Ya Ja Layi, Ya Bude Kofa ga Sauran Kungiyoyin Izalah
- Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci hadin kai tsakanin Musulmi kan taron 'Qur'anic Convention'
- A cikin wani bidiyo, Sheikh Bala Lau ya gargadi masu amfani da kafofin sada zumunta su guji furta maganganu marasa amfani
- Malamin ya jaddada cewa idan akwai matsala, suna da shirin dage taron, ya bukaci sauran kungiyoyin Musulunci su mara musu baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sake yin magana kan taron 'Qur'anic Convention' da za a yi.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci neman hadin kai daga sauran kungiyoyin Izalah da al'ummar Musulmi baki daya.

Asali: Facebook
'Qur'anic Convention': Bala Lau ya gargadi masu yada karya '
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Sheikh Bala Lau ya gargadi masu amfani da kafofin sadarwa su dakatar da rubutu kan lamarin idan ba alheri za su fada ba.
Malamin ya tabbatar da cewa yana da yakinin Ubangiji SWT zai taimake su saboda dominsa suke yi kuma ya isar musu.
"Ina fata daga yanzu a rufe wannan babi, an rufe maganar ko? Na san kuna da da'a.
"Ku yi hakuri duk wani abin da za a fada, ba ni so ko ba mu son mu sake jin wata magana.
"A daina rubuce-rubuce, a daina fadan wasu maganganu, idan dai don Allah muke yi yardarSa muke nema, to Ya isar mana."
- Sheikh Abdullahi Bala Lau
Bala Lau ya sha alwashin dage taron 'Qur'anic Convention'
Sheikh Bala Lau ya ce a shirye suke ko yanzu idan suka hararo akwai matsala za su dage wannan 'Qur'anic Convention' da ake shirin yi.
Daga bisani, Shehi ya shawarci sauran kungiyoyi da su ba su goyon baya domin tabbatar da hadin kai tsakanin Musulmi.

Kara karanta wannan
'Ku tuba kafin Ramadan': Dan ta'adda ya gargadi al'umma, ya fadi matakin da zai ɗauka
"Wannan kungiya ce mai neman hadin kai, duk abin ake son hada kan al'ummar Musulmi wajibi ne mu ba da mara masa baya.
"Wannan 'convention' da za a yi ya ishe ka, ka gane idan ka kwatanta shi da gasar Alkur'ani mai girma, mu kadai muke yi? a'a duk wani Musulmi ya shafe shi.
"Ina kira ga 'ya'yan kungiya da sauran Ahlus Sunnah su zo kofar mu a bude take, duk wani abu da zai hada kanmu muna maraba da shi da lale marhabun."
- Sheikh Bala Lau
Yadda malamai suka rabu kan taron 'Qur'anic Convention'
Kun ji cewa lamarin 'Quranic Convention' ya jawo ka-ce-na-ce tsakanin malamai da al'ummar Musulmi musamman a Arewacin Najeriya.
Sai dai wasu da ke goyon bayan taron sun kawo hujjoji domin kare shirin da kuma neman goyon bayan sauran bayin Allah cikin al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng