Sufetan 'Yan Sanda da Aka Kora daga Aiki na Fuskantar Hukuncin Kisa a Jihar Kano

Sufetan 'Yan Sanda da Aka Kora daga Aiki na Fuskantar Hukuncin Kisa a Jihar Kano

  • An gurfanar da tsohon sufetan ‘yan sanda, Isyaku, a babbar kotun Kano kan zargin kashe direba, Isyaku Ya’u, a Kwanar Dangora
  • Bayan yanke masa hukunci a gaban kwamitin bincike, an kori Isyaku daga aikin ‘yan sanda tare da tsare shi na watanni shida
  • Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba S/Dinki, ya kalubalanci bukatar beli, inda kotu ta dage shari’ar zuwa 24 ga Fabrairun 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da tsohon sufetan ‘yan sanda a gaban babbar kotun Kano mai lamba 22 kan kashe wani direba.

An kori sufeta Isyaku daga aikin ‘yan sanda bayan yanke masa hukunci a gaban kwamitin bincike kan harbe direban mai suna Isyaku Ya’u.

Tsohon sufetan 'yan sanda na fuskantar hukuncin kisa a Kano
An gurfanar da tsohon sufetan 'yan sanda a Kotu kan zargin kisan kai. Hoto: High Court
Asali: UGC

An gurfanar da tsohon sufeta a kotu

Kara karanta wannan

2027: Limami ya fadi abin da za a yiwa ƴan siyasar da ke sukar shari'ar Musulunci

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsohon dan sandan ya harbe direban har lahira a Kwanar Dangora a watan Afrilun 2021, lamarin da ya jawo fushin mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin kisan da ya yi wa direban ya jawo zanga-zanga a yankin, wanda ya kai ga tsare shi na tsawon watanni shida a hannun ‘yan sanda.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotun majistare, an dage shari’ar saboda rashin hurumin kotun, sannan aka tsare shi har zuwa wannan gurfanarwar.

Ana zargin sufetan da laifin kisan kai

Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba S/Dinki, ya tuhumi wanda ake zargin da laifin kisan kai, inda ya kalubalanci bukatar beli da lauyansa.

Tun da fari, lauyan wanda ake kara, Barista Najib Hamisu, ya gabatar da bukatar ba da belin Sufeta Isiyaku, amma bai yi nasara ba.

Mai shari’a Salma Danbaffa ta dage shari’ar zuwa ranar 24 ga Fabrairu domin ci gaba da sauraren karar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi bajinta, sun ceto fitaccen basarake bayan shafe kwanaki a wurin miyagu

An kori dan sanda mai karbar rashawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan Kano ta sallami wani kurtu, Ado Abba bisa zargin karɓar cin hanci daga jama’a a kan titi.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa akwai lokacin da Ado ya taba neman cin hanci a hannunsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.