2027: Limami Ya Fadi Abin da Za a Yiwa Ƴan Siyasar da Ke Sukar Shari'ar Musulunci

2027: Limami Ya Fadi Abin da Za a Yiwa Ƴan Siyasar da Ke Sukar Shari'ar Musulunci

  • An yi kira ga Musulmai a Kudu maso Yamma da su kauracewa duk ɗan takarar gwamna da ba zai goyi bayan kafa kotunan Musulunci ba
  • Sheikh Ridwan Jamiu ya bayyana kafa kotunan shari’a a matsayin haƙƙin doka, yana mai cewa lokaci ya yi da za a tabbatar da haka
  • Kundin tsarin mulki ya ba da izini na kafa kotunan shari’a domin warware al’amura kamar aure, rabuwa, da gadon dukiya, inji limamin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - An yi kira ga Musulmai a yankin Kudu maso Yamma da su ki zaben duk wani ɗan takarar gwamna da ba zai goyi bayan kafa shari'ar Musulunci ba.

Limamin babban masallacin Lekki, Sheikh Ridwan Jamiu, ne ya bayyana wannan yayin da ake muhawara kan batun kafa kotunan shari’a a yankin Yarbawa.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Ridwan Jamiu ya nemi Musulmai su kauracewa 'yan siyasar da ke adawa da kafa kotunan shari'a
Limamin Lekki ya nemi Musulmi su ki zabar 'yan takarar da ke adawa da kafa kotunan shari'a. Hoto: @LekkiMusUmmah
Asali: Twitter

Yayin hudubar Juma’a a masallacin Lekki, Sheikh Jamiu ya ce ya zama dole a riƙa tambayar ‘yan takara matsayinsu kan kafa kotunan shari’a, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dole dan takara ya amince da shari'a' - Limami

Ya yi kira ga Musulmai su yi tunani sosai kan zaɓe, yana mai cewa, “Dole ne duk wanda yake neman kuri’unku ya himmantu wajen kafa kotunan shari’a.”

Sheikh Jamiu ya bayyana cewa kafa kotunan Shari’a a Kudu maso Yamma na daga cikin haƙƙin doka, yana mai cewa lokaci ya yi da za a tabbatar da wannan.

“Lokaci ya yi da za mu nemi haƙƙinmu na doka. An dade ana jiran kafa kotunan shari’ar Musulunci a jihohin Kudu maso Yamma,” inji limamin.

'An ambaci shari'a sau 73 a kundi' - Limami

Ya bada misalai daga kundin tsarin mulki, inda doka ta amince da shari’a, yana ambaton sashe na 38 da 40 da suka ba da ‘yancin addini.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji

Punch ta rahoto Sheikh Jamiu ya ce an ambaci kalmar shari’a kusan sau 73 a cikin kundin tsarin mulki na Najeriya.

Ya kuma yi karin haske cewa kotunan shari’a za su kasance kamar hanyar sulhu (ADR) da ake amfani da ita wajen magance matsaloli da suka shafi aure, saki, gado, da sauransu.

Kafa shari'a: Rigima ta kunno kai a Kudu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rigima ta kunno kai a yankin Kudu maso Yamma kan shirin kafa kotunan shari’ar Musulunci a jihohin yankin.

Yayin da Kirista da masu addinin gargajiya ke adawa da kafa shari'a a jihohin Yarbawa, Musulman yankin sun ce babu gudu babu ja da baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.