Wani direba ya halaka jami'in 'dan sanda a Legas
- An gurfanar da wani direba gaban kotu bisa laifin kashe wani dan sanda a jihar Legas
- Direban mai suna Abdulkareem Shuaibu ya musanta aikatan laifin yayin da ya gurfana gaban kotu
- Alkalin kotun ta bayar da belin sa kan kudi N500,000 kuma ta dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Afrilu
A ranar Laraba 7 ga watan Maris ne aka gurfanar da wani direba mai suna Abdulkareem Shuaibu a gaban Kotun Majistare na Ebute Meta bisa laifin tukin ganganci da yayi sanadiyar mutuwar wani jami'in dan sanda mai mukamin sajent.
Ana tuhumar Shuaibu da aikata laifuka guda uku wanda suka hada da tukin ganganci, tuki ba tare da lasisi ba da kuma laifin kisar jami'in dan sanda.
Laifin da ya ci karo da sashi na 20, 28 da kuma 36 (1) na Road Traffic Act, A dokokin Jihar Legas na 2012.
KU KARANTA: Gumi ya bayyana hanya daya tilo da sojoji za su bi don cin galaba kan Boko Haram
Sai dai wanda ake tuhuma bai amince da aikata laifin ba.
Dan sanda mai shigar da kara, Kehinde Olatunde ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Maris misalin karfe 2.45 na dare a kasuwar Ijora Olopa.
Ya kara cigaba da cewa Shuaibu yayi amfani da motar sa kirar Passat mara rajista inda ya bige Sajent Oshodi, wanda jami'in Hukumar yan Sanda ne da ke aiki da sashi masu kawo daukin gagawa na RRS da ke Alausa a Ikeja.
Alkalin kotun, Majistare Bola Folarin Williams ta bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa.
Ta kuma dage sauraron karar har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng