"Ba Ku da Tabbas": Gwamna Ya Ja Kunnen Mukarraban Gwamnati, Ya ba Su Shawara

"Ba Ku da Tabbas": Gwamna Ya Ja Kunnen Mukarraban Gwamnati, Ya ba Su Shawara

  • Gwanmnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya yi hannunka mai sanda ga masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa
  • Caleb Mutfwang ya gayawa muƙarraban gwamnatin tasa cewa kujerunsu ba su da tabbas, don haka akwai buƙatar su zage damtse
  • Ya buƙace su da su yi aiki tuƙuru wajen ganin sun kawo ci gaba wanda al'ummar jihar za su amfana da shi a mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi muhimmin kira ga mutanen da ya ba muƙamai a gwamnatinsa.

Gwamna Mutfwang ya buƙaci dukkan mutanen da ya ba muƙamai da su ƙara himma tare da yin aiki tuƙuru domin yin abin da ya dace.

Gwamnan Plateau ya gargadi mukarraban gwamnati
Gwamna Caleb Mutfwang ya gargadi mukarraban gwamnati Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan kira ne a yayin taron bita da aka shirya domin muƙarraban gwamnati a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bayan yin garambawul, gwamnan Nasarawa ya nada sababbin kwamishinoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Plateau ya ja kunnen muƙarrabansa

An gudanar da taron ne a garin Miango, da ke cikin ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateaj, inda kwamishinoni, manyan sakatarori, mashawarta na musamman, da wasu jami’an gwamnati suka halarta.

Gwamna Mutfwang ya jaddada cewa banda shi da mataimakinsa, babu wani mai muƙami wanda aikinsa yake da tabbas.

"Babu lokacin nuna son kai, saboda ɗaya daga cikin abin da za mu yi shi ne kawo ci gaba ga al'umma."
"Babu wanda zai iya yin hakan shi kaɗai, don haka lokacin da mutane za su riƙa ba kansu cikakken iko ya ƙare."
Yanzu lokaci ya yi da za mu haɗa kai mu yi amfani da wannan damar. Ka da ku yi tunanin kuna da isashshen lokaci, ko da a ce bai fi wata uku da kai mutum ma'aikata ba, ya tabbatar ya yi abin da ya dace."
"Dukkaninmu, bayan ni da mataimakin gwamna, babu wanda kujerarsa take da tabbas. Ku yi ƙoƙari a dukkanin matsayin da kuka samu kanku sannan ku yi gaskiya."

Kara karanta wannan

2027: Limami ya fadi abin da za a yiwa ƴan siyasar da ke sukar shari'ar Musulunci

"Eh yana da kyau ku yi min biyayya, amma daga yanzu abin da na ke so shi ne biyayyarku ta koma ga Allah."

- Gwamna Caleb Mutfwang

Gwamnan Plateau ya kori kwamishinoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang ya yi sallama a majalisar zartarwar jihar.

Gwamna Caleb Mutfwang ya sallami wasu kwamishinoni guda biyar da ke aiki a gwamnatinsa daga kan muƙamansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng