Gwamna Ya Tura Manyan Motocin Buldoza, An Rusa Fitacciyar Kasuwa da Tsakar Dare
- Gwamnatin jihar Filato ta rusa babbar kasuwar Ƴankeke da ke kusa da asibitin koyarwa na jami'ar Jos watau JUTH
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar JMDB sun isa kasuwar da daddare tare da manyan motocin buldoza, suka rusa shagunan mutane
- Ƴan kasuwa sun bayyana mamakinsu da rusau ɗin, inda suka roƙi gwamnatin Filato da ta biya su diyyar dukiyar da suka yi asara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Gwamnatin jihar Filato karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang ta shammaci ƴan kasuwa a fitacciyar kasuwar Yankeke da ke birnin Jos.
Hukumar raya birnin Jos (JMDB) ta rusa kasuwar Yankeke da ke kusa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

Asali: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kasuwar na dauke da masu sayar da keken hawa, kayan abinci, tufafi, da sauran kayan kasuwanci.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rusa kasuwar ba zato ba tsammani
Shaidun gani da ido sun ce jami’an JMDB sun isa kasuwar da misalin karfe 11:30 na dare da babbar motar rusau, inda suka fara rushe shaguna tare da lalata dukiya ta miliyoyin Naira.
Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga babban manajan hukumar JMDB, Hart Bankart.
Mataimakin shugaban kasuwar, Sadik Aliyu ya ce har yanzu suna kan shari’a da JMDB, don haka sun yi matukar mamakin rusau din.
Ƴan kasuwa sun shiga kotu
Sadiƙ ya ce:
"Kotu ta yanke hukunci a baya cewa mu sabunta haya tare da sake gina shagunanmu. Amma bayan sabuwar gwamnati ta hau, sai suka sake kai mu kotu.
"Duk da cewa an yanke hukuncin da ya ba su gaskiya amma mun daukaka kara, kuma mun mika musu takardar karar. Abin mamaki, da daddare sai suka zo suka rusa kasuwa, suka lalata dukiyarmu mai tarin yawa."

Kara karanta wannan
Boko Haram ta bullo da sabuwar dabarar kashe bayin Allah, an hallaka mutane a Borno
Wasu ‘yan kasuwa sun bayyana irin asarar da suka tafka, suna masu cewa sun rasa hanyar samun abincinsu, kuma sun roki gwamnati ta biya su diyya.
Yan ƙasuwar sun tafka asara
Emmanuel Dung, wani mai sayar da keke, ya bayyana takaicinsa da cewa:
“Mun samu saɓani da hukumar JMDB, amma kafin mu warware lamarin, sai suka zo cikin dare suka rusa shagunanmu.
Wannan keke da nake riƙe da shi kadai yana da darajar Naira miliyan 1.5, kuma sun lalata shi. Mu ne muka zabe su, amma yanzu ga irin abin da suke mana.”
‘Yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta duba halin da suke ciki sannan ta biya su diyya, domin suna cikin mawuyacin hali na matsin rayuwa.
Gwamna ya musanta hana kiran sallah
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato musanta raɗe-raɗin cewa gwamnatinsa ta haramta kiran sallah.
Gwamnan ya ce zai gudanar da bincike kan lamarin amma babu wanda ya hana kiran sallah a jihar Filato, magana ce ta ƴan shaci faɗi.
Asali: Legit.ng