Gwamna Bago Ya Yi Ruwan Miliyoyi a Taron Izala na Neman Naira Biliyan 1.5
- Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya ba da gudunmuwar miliyoyin Naira ga ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS)
- Mohammed Umaru Bago ya bayyana hakan ne yayin taron ƙasa na shekara-shekara da ƙaddamar da asusun bunƙasa ilimi na ƙungiyar a Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa manyan mutane ciki har da ministoci da malamai daga Najeriya da ketare sun halarci taron tare da bayar da gudunmuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An gudanar da babban taron ƙasa na shekara-shekara na ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS) da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya jagoranta a Abuja.
A yayin taron, Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya ba da tallafin miliyoyin Naira domin taimakawa ƙungiyar wajen cimma manufofinta na yaɗa addinin Musulunci da bunƙasa ilimi.

Asali: Facebook
Kakakin gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 9 ga Fabrairu, 2025 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Umaru Bago ya ba Izala N10m
Wakilan gwamnatin jihar Neja sun halarci taron ƙasa na shekara-shekara na ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a birnin Abuja.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 domin taimaka wa ƙungiyar wajen gudanar da muhimman ayyukanta na addini da ci gaban ilimi.
Darakta Janar na Hukumar Harkokin Addini a jihar Neja, Malam Umar Faruk Abdullahi, wanda ya wakilci Gwamna Bago, ya jinjinawa ƙungiyar bisa rawar da take takawa wajen yaɗa addini.
Gwamnan Neja ya bukaci a yi wa kasa addu’a
Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙungiyar domin ganin ta cimma burinta na ƙarfafa addinin Musulunci da ilimi.
Ya yi kira ga malaman addini da su ci gaba da yin wa’azin zaman lafiya tare da yin addu’o’i domin zaman lafiyar Najeriya da ci gaban ƙasa.
Malam Umar Faruk Abdullahi ya bayyana cewa gudunmuwar da Gwamna Bago ya bayar alama ce ta jajircewarsa wajen tallafa wa harkokin addini da ilimi a jihar Neja da ƙasa baki ɗaya.
Manyan mutane sun halarci taron Izala
Taron ya samu halartar manyan malamai da jami’an gwamnati daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashen waje.
Cikin manyan baki da suka halarci taron har da ministoci da shahararrun malaman addini waɗanda suma suka bayar da gudunmuwar kuɗi domin tallafa wa ayyukan ƙungiyar.
Sheikh Isa Ali Pantami na cikin manyan malam Najeriya da suka halarci taron da gabatar da jawabi na musamman ga mahalarta taron.
Limamin Abuja ya yi nasiha ga malamai
A wani rahoton, kun ji cewa sabon limamin masallacin kasa da ke Abuja ya yi kira ga malamai da su nisanci riciki a kafafen sadarwa.
Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu ya kuma yi kira ga al'ummar Musulmi da su fara shirin tunkarar watan Ramadan da ke matsowa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng