'An Yi Son Rai a Zaben Sabon Sarki': Yarima Ya Cire Tsoro, Ya Maka Gwamna a Kotu

'An Yi Son Rai a Zaben Sabon Sarki': Yarima Ya Cire Tsoro, Ya Maka Gwamna a Kotu

  • Prince Ismaila Owoade ya garzaya kotu, yana son a soke nadin Prince Abimbola Owoade a matsayin Alaafin na Oyo saboda ba bisa ka’ida ba
  • Ya ce bai kamata a nada wani ba tare da Baba Iyaji ya gabatar da sunan wanda ya dace ga masu ikon nadin sarki, matau Oyo Mesi ba
  • Kotun ta sanya 11 ga Maris, 2025, don sauraren karar, yayin da Prince Gbadegesin ke kalubalantar matakin Gwamna Seyi Makinde

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Dan takarar sarautar Alaafin na Oyo, Prince Ismaila Olamilekan Owoade, ya maka Gwamna Seyi Makinde da wasu mutum 19 a kotu.

Prince Ismaila ya zargi wadanda ya ke karar da cire shi daga suna wadanda ke neman kujerar, inda ya ce an nada Prince Abimbola Owoade ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

'Binani ce ta ci zaɓen Adamawa': Hudu Ari ya yi rantsuwa an tilasta shi game da Fintiri

Princve Ismaila Owoade ya maka gwamnan Oyo da wasu mutum 19 a kotu.
Nadin sabon Alaafin na Oyo ya jawo an maka gwamna da wasu mutum 19 a kotu. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Facebook

Lauyan Owoade, Bamidele Ogundele, ya shigar da karar a gaban Mai shari’a Jimoh Adesina na Babbar Kotun Jiha dake Oyo, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Prince Ismail na so a soke nadin Alaafin

Yayin da kotun ta sanya ranar 11 ga Maris domin fara sauraren karar, Ismaila na so a hana Prince Abimbola da Prince Lukman Gbadegesin kiran kansu a matsayin Alaafin.

Wanda ke karar yana neman kotu ta soke nadin Prince Abimbola a matsayin Alaafin, yana cewa ba a bi 'dokokin Nadine' na 1961 da 2000 ba.

Baya ga gwamna, Prince Ismail ya hada da kwamishinan shari’a, kwamishinan harkokin masarauta, da wasu manyan sarakunan Oyo a cikin wadanda yake kara.

Rahoto ya lissafa wadanda Yarima ke kara

Hakazalika, Prince Ismail ya sanya Basorun Oyo, Agbaakin, Iba Samu, Mogba, da wasu manyan sarakuna guda 20 a matsayin wadanda ake kara.

Owoade ya bayyana cewa wadanda aka nada basu cike ka’ida ba, inda aka ki tuntubar Baba Iyaji, wanda yake da alhakin gabatar da sunayen ’yan takara.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Gwamna ya kaɗu da mai martaba sarki ya riga mu gidan gaskiya

Ya ce Baba Iyaji ya kamata ya tantance 'yan takara bisa ka'idoji kafin gabatar da sunayensu ga Oyo Mesi da sauran masu ruwa da tsaki.

Prince Ismaila ya nemi kotu ta umurci masu nadin sarki da su yi amfani da tsarin Baba Iyaji, tare da nada shi a matsayin Alaafin na Oyo saboda shi ya fi cancanta.

Gwamna ya mika sanda ga sabon sarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Seyi Makinde ya miƙa sandar mulki ga sabon Alaafin na Oyo, Abimbola Akeem Owoade, a fadar gwamnati.

Kwamishinan labarai na Ooyo ya ce zaben sabon Alaafin ya biyo bayan dogon nazari da shawarwari don tabbatar da cigaban masarautar da al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.