Rikicin Sarauta: Gwamna Ya Shiga Matsala, An ba Shi Wa'adin Kwanaki 30 Ya Tsige Sarki

Rikicin Sarauta: Gwamna Ya Shiga Matsala, An ba Shi Wa'adin Kwanaki 30 Ya Tsige Sarki

  • Masu zaɓen Alaafin da Yarima Lukman Gbadegesin sun ba Gwamna Seyi Makinde wa’adin kwanaki 30 ya soke nadin Akeem Owoade
  • Sarakunan Oyomesi sun musanta zargin gwamnan cewa an aikata cin hanci a tsarin zaben, tare da kalubalantarsa ya gabatar da shaida a kotu
  • Sun yi ikirarin cewa zaben Alaafin aiki ne na Oyomesi kawai, ba na gwamna ba, suna mai zargin Makinde da karya dokar nadin Alaafin ta 1961

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo - Sarakuna biyar daga cikin masu alhakin zaɓen sabon sarki a jihar Oyo sun ba Gwamna Seyi Makinde wa'adin wata guda ya soke naɗin Alaafin.

Masu zaɓen sarkin dai sun gimdaya wa'adin ne karƙashin jagorancin Basorun na Oyo, Mai martaba Yusuf Ayoola, tare da dan takararsu da suka fi so, Yarima Lukman Gbadegesin.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

Sabon Alaafin na Oyo.
Sarakuna 5 sun bukaci Gwamna Seyi Makinde ya soke naɗin sabon Alaafin Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Sarakuna sun ba gwamna wa'adin wata guda

Sun bai wa Gwamna Seyi Makinde wa’adin kwanaki 30 ya soke nadin Akeem Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin masarautar Oyo, musamman tsakanin sarakunan da ke ikirarin cewa nadin bai bi ka’idar da ta dace ba.

Sarakunan, tare da Yarima Gbadegesin, sun yi barazanar daukar matakin shari’a idan gwamnan ya gaza soke naɗin Alaafin da ya yi ba kan ƙa'ida ba.

Sun bayyana cewa sun damu matuka kan zargin da gwamnan ya yi na cewa an yi cin hanci da rashawa yayin gudanar da tsarin zaben sabon Alaafin.

Masu zaɓen Alaafin sun gargaɗi Makinde

Har ila yau, sun gargadi gwamnan kada ya kara yin wasu kalamai da za su bata musu suna ko kuma yi wa tsarin zaben kazafi.

A baya-bayan nan, Gwamna Makinde ya nada Akeem Owoade a matsayin sabon Alaafin, matakin da wasu daga cikin sarakunan Oyomesi suka yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga yanayi da yayan gwamna ya riga mu gidan gaskiya

A cewarsu, gwamnan ya yi watsi da Yarima Lukman Gbadegesin, wanda suka zaba bisa doka da ka’ida.

Sun bayyana cewa tsarin da ya kai ga nasarar Gbadegesin ya kasance mai cike da gaskiya da adalci, kuma ba a samu wata shaida ta cin hanci ba.

Saboda haka, sun kalubalanci gwamnan ya gabatar da wata shaida a kotu don tabbatar da zargin da ya yi na cewa sun karɓi na goro kafin zaɓen sabon Alaafin.

An zargi gwamnan Oyo da ketare huruminsa

Sarakunan sun kuma yi ikirarin cewa Gwamna Makinde ya ketare huruminsa wajen nada Owoade, a cewarsu zaben Alaafin aiki ne na Oyomesi kaɗai bisa doka da al’ada.

Masu alhakin zaɓen basaraken sun dage cewa gwamnan ba shi da ikon tsoma baki cikin wannan al’amari, cewar rahoton Premium Times.

Lauyan Gbadegesin, Kunle Sobaloju (SAN), ya kuma zargi gwamnan da karya hukuncin kotu ta hanyar dogaro da shawarar Ifa wajen yin nadin, wanda ya saba wa dokar nadin Alaafin ta 1961.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya jajanta da Malamin Musulunci, yayan gwamna suka kwanta dama

Bisa waɗannan dalilai ne masu zaɓen Alaafin biyar suka bai wa Gwamna Makinde wa'adin kwanaki 30 ya soke naɗin Akeem Owoade a matsayin Alaafin.

EFCC ta gayyaci sarakuna 7 a Oyo

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta gayyaci wasu daga cikin masu naɗin Alaafin bisa zargin karɓar rashawa.

Mai magana da yawun EFCC ya tabbatar da wannan lamari, ya ce wasu daga ciki sun masa gayyatar, sauran kuma za su kai kanso ofishin hukumar a makon nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262