Rashin Imani: Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Dan Majalisa bayan Karbar N100m
- Ana ci gaba da samun bayanai daga wajen ƴan bindigan da suka kashe ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Justice Azuka
- Miyagun waɗanda suka shigo hannu, sun bayyana cewa sun cire N100m daga asusun 'dan siyasar, kafin daga bisani su hallaka shi
- Rundunar ƴan sandan jihar Anambra dai ta tabbatar da cafke mutane tara da ake zargi suna da hannu a aika-aikar kashe ɗan majalisar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Ƴan bindigan da suka sace ɗan majalisar dokokon jihar Anambra, Justice Azuka, sun yi bayani bayan sun shiga hannun jami'an tsaro.
Ƴan bindigan sun bayyana cewa sun cire N100m daga asusunsa kafin su kashe shi har lahira.

Asali: Facebook
Ƴan bindiga sun kashe ɗan majalisa a Anambra
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ɗaya daga cikin ƴan bindigan da aka cafke ne ya bayyana hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an ƴan sanda sun tabbatar da kama mutane tara da ake zargi da sacewa tare da kisan Justice Azuka, rahoton Channels tv ya tabbatar.
An dai gano gawar ɗan majalisar wacce ta fara ruɓewa a kusa da gadar Neja ta biyu, a Onitsha, jihar Anambra da safiyar Alhamis, kwanaki 44 bayan sace shi.
Wasu ƴan bindiga guda huɗu ɗauke da makamai ne suka sace shi bayan sun kai masa farmaki a Ugwunabamkpa, Onitsha a daren Kirsimeti.
Yadda ƴan bindiga suka karɓi N100m
A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ya bayyana cewa, sun harbe Justice Azuka ne a washegarin ranar Kirismeti bayan sun cire N100m daga asusunsa.
Wanda ake zargin ya shaidawa masu bincike cewa sun harbe shi har sau biyu a kansa kafin ya mutu.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Nnaghe Itam, ya ce an kama mutane tara da suka taka muhimmiyar rawa a wannan aika-aika.
Ƴan sanda sun cafke waɗanda ake zargi
Daga cikin waɗanda aka kama, akwai mutum biyu waɗanda ba su kai shekara 20 ba, yayin da mafi girma daga cikinsu bai wuce shekara 30 ba.
Itam ya bayyana sunayensu kamar haka: Ugochukwu Onuorah (30), Ikemefuna Ossai (20), Ikenna Orugu (27), Chibuike Obiefuna (19), Chinonso Olisa (19).
Sannan akwai Chinedu Okoli (21), David Ojini (25) da Peter Sunday (20) wanda aka bayyana a matsayin mafi shahara a cikinsu.
Kwamishinan ƴan sandan ya ce jami’ansa tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta jihar ne suka cafke waɗanda ake zargin.
Jami'an tsaro sun ragargaji ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na rundunar Agunechemba a jihar Anambra, sun yi wa ƴan bindiga raga-raga.
Jami'an tsaron tare da haɗin gwiwar dakarun sojoji sun hallaka ƴan bindiga bayan sun kai farmaki a maɓoyarsu da ke cikin daji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng