Reno Omokri: Fasto Ya Jinjinawa Annabi Muhammad SAW, Ya Yabawa Musulmai
- Fitaccen masanin addinin Kirista, Reno Omokri ya bayyana cewa tun kafin ya shiga siyasa yake girmama Musulunci da Musulmi
- Fasto Reno Omokri ya ce Musulunci addini ne da yake da cikakkun ka’idoji da mafita ga dukkan bangarorin rayuwar dan Adam
- Omokri ya jaddada cewa mutunci da kyawawan halaye suna taka rawa mai muhimmanci wajen kawo zaman lafiya a kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fitaccen dan siyasa, malami kuma marubuci, Reno Omokri, ya bayyana dalilan da suka sa yake girmama Musulunci da Annabi Muhammad (SAW) duk da cewa shi ba Musulmi ba ne.
Faston ya ce tun kafin ya shiga harkar siyasa yake da wannan fahimta, yana mai cewa Musulunci yana da tsari da ka’idoji masu bayani kan komai tun daga haihuwa har zuwa mutuwa.

Asali: Facebook
Reno Omokri ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a Facebook, inda ya yi nuni da cewa musulmi na daraja Annabi Muhammad (SAW) fiye da yadda wasu mabiya addinai ke girmama shugabanninsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musulunci a matsayin tsarin rayuwa
Reno Omokri ya ce daya daga cikin abubuwan da suka burge shi a Musulunci shi ne yadda yake da ka’idoji kan dukkan bangarorin rayuwa.
Ya bayyana cewa tun daga yadda mutum zai tashi daga barci, yin sallah, yin wanka, cin abinci, zuwa yadda ake gudanar da aure da zamantakewa, Musulunci ya yi cikakken bayani.
Hakazalika, ya ce Musulunci na da tsarin da ke koyar da yadda za a tafiyar da dukiya da kuma yadda za a shawo kan talauci.
Ya ce wannan tsari yana bai wa Musulmi damar samun nutsuwa da daidaito a rayuwarsu, kasancewar addinin na zama musu cikakken jagora.
Batun girmama Annabi Muhammad (SAW)
Reno Omokri ya bayyana cewa Musulmi suna girmama Annabi Muhammad (SAW) fiye da yadda wasu Kiristoci ko Yahudawa ke daraja shugabanninsu.
Ya ce yana da matukar wahala a ji Musulmi yana ambaton sunan Annabi Muhammad (SAW) cikin fushi ko izgili.
Bugu da kari, ya bayyana yadda wasu Kiristoci ke ambaton sunan Annabi Isa (AS) ko Musa (AS) cikin zancen banza, abin da ya ce yana nuna rashin girmamawa.
Bukatar fahimtar juna da zaman lafiya
A cewarsa, daya daga cikin manyan matsalolin duniya shi ne rashin fahimtar juna tsakanin addinai daban-daban.
Ya ce wasu Kiristoci sun kulle zukatansu daga fahimtar Musulunci da abubuwan da suka shafi Musulmai.
Ya kawo misalai daga tarihin duniya, yana mai cewa akwai lokutan da Musulmi suka taimaka wa Kiristoci fiye da yadda Kiristoci suka taimaki junansu.
Misali, ya ambato yadda Imam Abubakar Abdullahi ya ceci Kiristoci 262 a lokacin rikicin Barkin Ladi.
Ya kuma yi maganar yadda Musulman daular Usmaniyya suka bai wa Yahudawa mafaka bayan an kore su daga Sifen a shekarar 1492.
Limamin Abuja ya yi nasiha ga malamai
A wani rahoton, kun ji cewa sabon limamin masallaci kasa na Abuja ya yi nasiha ga malamai kan sukar juna a kafafen sadarwa.
Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu ya ce bai kamata a rika samun gaba tsakanin malamai ba musamman a kafafen sada zumunta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng