Kungiyar CAN Ta Karrama Wani Limami Akan Ceton Kiristoci 200 Da Ya Yi a Plateau

Kungiyar CAN Ta Karrama Wani Limami Akan Ceton Kiristoci 200 Da Ya Yi a Plateau

  • Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta karrama Abdullahi Abubakar a ranar Asabar
  • Limamin ya ceci kiristocin 200 daga wani farmaki da ‘yan bindiga su ka kai mu su
  • Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato

FCT, Abuja - Kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN ta karrama wani limami, Abdullahi Abubakar, wanda ya ceci kiristoci 200 daga wani farmakin da aka kai musu a karamar hukumar Barkin Ladi dake jihar Filato.

Shugaban CAN, Dr Samson Olasupo Ayokunle ne ya mika tambarin karramawan ga Imam Abubakar a ranar “Sapphire CAN Day” na shagalin cikar CAN shekaru 45 da suka yi ranar Asabar da daddare a Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar CAN Ta Karrama Wani Limami Akan Ceton Kiristoci 200 Da Ya Yi a Plateau
Abudullahi Abubakar da David Young. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Limamin ya bawa mutane 200 mafaka ya ceci rayuwarsu

Kara karanta wannan

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Limamin ya ceci fiye da mutane 200 ne a ranar 24 ga watan Yunin 2021 yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka afka wa anguwanni 15 da ke karamar hukumar Barkin Ladi inda suka halaka fiye da mutane 200.

Daily Trust ta ruwaito yadda gwamnatin Amurka a watan Yulin 2019 ta taba karrama wani malamin addinin musulunci mai shekaru 83 tare da wasu shugabanni 4 daga Sudan, Iraq, Brazil da Cyprus.

Yayin jawabi a taron, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, wanda shi ma aka karrama a taron ya bukaci kiristoci da sauran shugabannin addinai dake fadin Najeriya su dinga wa’azi cikin adalcin da bin dokokin kasa.

Kamar yadda ya ce:

“Don neman zaman lafiya da hadin kan al’umma, wajibi ne kungiyar kiristoci da shugabannin addinai a Najeriya su yi wa’azi akan adalci da hadin kai a ko yaushe kuma kada kowa ta takura wa kowa a wurin bauta.”

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

A cewar sa hakan ne zai kawo hadin kai da zaman lafiya a cikin kasa. Ya hori shugabannin kiristoci su yi kokarin yaki da duk wani abu da zai kawo rabuwar kawuna.

A cewar sa:

“Muna alfahari da yadda CAN da sauran kungiyoyin addinai suke taka rawar gani a kasar mu.
“Ina sane da yadda shugabannin addinin musulunci da sauran addinai suke gyara tsakanin al’umma ta hanyar dakatar da fadace-fadace tsakanin jama’a.”

Yayin da shugaban kungiyar CAN yake gabatar wa da mataimakin shugaban kasa alamar jinjinawa, ya ce sun karrama shi ne sakamakon yadda ya dade yana kokari a jihohi har da kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164