Diyar Gwamnan jihar Kano, Ganduje ta zama Malama, ta na zuba wa’azi da ayoyin Kur’ani

Diyar Gwamnan jihar Kano, Ganduje ta zama Malama, ta na zuba wa’azi da ayoyin Kur’ani

  • An ga ‘Yar gwamnan jihar Kano, Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta na wa’azi a shafin Facebook
  • Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta fadakar da mutane a game da jarrabawar Allah (SWT)
  • Irinsu tsohon kwamishina, Injiniya Muaz Magaji sun tofa albarkacin bakinsu, yace Allah ya sa a daure

Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta fito ta na yin wa’azi a wani bidiyo. Wannan lamari ya jawo mutane su na ta magana a dandalin sada zumunta.

Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje wanda ke rike da sarautar Fulanin Zannan Laisu na kasar Fika, ta fadakar da mutane game da jarrabawar Ubangiji (SWT).

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Daily Nigerian Hausa, an ‘Diyar mai girma gwamnan ta Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta na fadakar da al’umma.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

Za a ji Asiya Balaraba-Ganduje ta jawo ayoyi daga suratul Taghabun da Baqarah daga littafi mai tsarki, ta na bayanin yadda Allah (SWT) yake jarabtar bayinSa.

“Akwai jarrabawa kala-kala da Allah (SWT) yake jarabtar bayinSa da shi. A suratul Taghabun Allah yace: “Babu wata annoba da za ta faru sai da izinin Allah (SWT). Duk wanda ya yi imani (a kan hakan), Allah zai shiryar da zuciyar shi, ya ba shi natsuwa da kwanciyar hankali. Kuma Allah (SWT) masani ne a kan komai. - Asiya Balaraba Ganduje.
Diyar Gwamnan jihar Kano
Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje Hoto: @asiyabalarabaganduje
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan malama ta cigaba da yin wa’azinta, tace haka zalika a cikin suratul Baqarah a aya ta 155 zuwa 157, Allah madaukakin Sarki yace zai jarabci bayinsa.

Me mutane su ke cewa?

Tuni mutane suka fara maidawa Fulanin Zanna Laisu Fika martani. Daga cikinsu har da tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Injiniya Mu’az Magaji.

Kara karanta wannan

Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin

Mu’az Magaji ya zo shafinsa ya rubuta:

“Ana hege a Kano...Na ji first Family a Kano sun fara Wa'azi...Allah SWT yasa an fara a Sa'a......Allah Yasa ya zama sanadin shiriya ne....Ammah...”

Amma wadanda suka saba bibiyar Asiya Balaraba-Ganduje a shafinta na Facebook, sun san ta saba fadakar da al’umma da yin irin wadannan wa’azi bini-bini.

An ruguza zaben tsagin Ganduje

Kotun ta zartar da cewa shugabannin da aka zaba na bangaren Ibrahim Shekarau ne halatattun shugaban APC a Kano, sannan ta dakatar da tsagin gwamnati.

Babban lauyan gwamnatin jihar Kano, kuma kwamishinan shari'a, Musa Lawan, ya ce su na nazari kuma za su daukaka kara game da hukuncin da aka zartar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel