Sarki Ya Shiga Babbar Matsala bayan Ya Zagi Dattijo, An Gurfanar da Shi a Kotu

Sarki Ya Shiga Babbar Matsala bayan Ya Zagi Dattijo, An Gurfanar da Shi a Kotu

  • Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ogun ta gurfanar da dakataccen sarkin Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi kan cin mutuncin wani dattijo
  • Ƴan sandan sun gurfanar da shi a kotun Majistire da ke Ifo kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da cin zarfi da aikata laifin da ka iya tunzura jama'a
  • Tun farko gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da basaraken tare da ƙwace duk wasu abubuwa da ke nuna cewa shi sarki ne har sai an gama shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - An gurfanar da sarkin gargajiya na Orile Ifo da aka dakatar, Oba Abdulsemiu Ogunjobi, a gaban kotun majistare ta Ifo a jihar Ogun.

Rundunar ƴan sanda ta gurfanar da basaraken ne yau Talata, tana tuhumarsa da aikata laifuffuka uku da suka haɗa da haɗa kai, cin zarafi da yunƙurin tayar da fitina a cikin jama'a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun yi awon gaba da fasinjoji zuwa daji

Sufetan yan sanda.
Yan sanda sun gurfanar da basaraken da ya ci mutuncin dattijo a gaban kotu Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rahoton Channels tv ya tattaro cewa hakan na zuwa ne bayan gwamnantin Ogun ta dakatar da sarkin kan zargin yin abin da bai dace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifin sarkin ya aikata a Ogun?

Gurfanar da Oba Abdulsemiu ya biyo bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, wanda ke nuna sarkin yana cin mutunci da zagin wani dattijo mai suna Areola Abraham, har yana masa barazanar kisa.

Oba Abdulsemiu Ogunjobi ya sha suka daga jama’a bayan bayyanar bidiyon da ke nuna yana cin mutunci da duka ga daya daga cikin masu sarauta, Arinola Abraham.

A cikin bidiyon na tsawon minti biyu, an ga Arinola yana durƙushe a kan titi, yayin da wani mutum da aka ce sarkin ne ke zagin shi da iyalansa, tare da zarginsa da hada kai don yin wani abu.

Sarkin, wanda tsohon ɗan sanda ne, ya yi ikirarin yana da ƙarfin faɗa a ji wajen jami'an tsaro, inda ya yi barazanar jefa dattijon cikin gidan yari.

Kara karanta wannan

Siyasar Kaduna: Bayan El Rufa'i, Ashiru Kudan ya yi rubdugu ga Uba Sani

Gwamnatin Ogun ta dakatar da basaraken

Tun da farko, gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Ogunjobi na tsawon watanni shida saboda abin da ta kira "halayya maras dacewa."

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar, Ganiu Hamzat, ya ce an dakatar da Ogunjobi ne saboda halayensa ba su dace da matsayin sarki ba.

Ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin kare martabar mutane da kuma tabbatar da darajar masarautu.

A cewar Ganiu Hamzat, an yanke wannan hukunci ne bayan da aka gayyaci sarkin da ake zargin ya aikata laifin zuwa ma'aikatar don bincike.

"Bayan bincike da aka gudanar kan lamarin, an dakatar da Oba Abdulsemiu Ogunjobi. An kwace dukkan abubuwan da ke nuna sarautarsa a matsayin Olorile na Orile-Ifo har sai an kammala bincike."

Kotu ta bayar da belin sarkin a Ogun

Bayan haka ne yan sanda suka kama sarkin tare da gurfanar da shi a gaban kotu, wacce daga bisani ta bayar da belinsa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama motar makamai da ake zargi za a mika ga 'yan bindiga

Haka nan kuma kotun ta ɗage sauraron shari'ar basaraken zuwa ranar 6 ga watan Maris, 2025, kamr yadda The Nation ta kawo.

Babbar kotu ta tsige basarake daga sarauta

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun Ogun mai zama a Abeokuta ta soke naɗin Mai martaba Alexander Macgregor a matsayin Olu na Ilawo.

Kotu ta soke naɗin basaraken ne bayan ta gamsu da hujjojin masu ƙara cewa ba a bi matakan da doka da shinfiɗa ba wajen naɗa sabon sarkin Ilawo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262