Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Nade, Mutane 29 Sun Samu Manyan Mukaman Gwamnati
- Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sababbin manyan sakatarori da kwamishinonin RMAFC a wani biki da aka gudanar a birnin Abuja
- Sababbin jami’an da aka rantsar sun fito daga jihohin Najeriya daban-daban, kuma an yi bikin ne kafin fara taron majalisar zartarwa
- Tinubu ya bukaci sababbin jami’an da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu domin ciyar da kasar gaba ta fuskar ci gaban shugabanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sababbin sakatarori takwas da kwamishinonin RMAFC 21.
An gudanar da bikin rantsarwar a cikin ɗakin taro na majalisar zartarwa ta tarayya da ke fadar shugaban kasa, Abuja, kafin fara taron FEC na farko a 2025.

Asali: Twitter
An rantsar da sakatarorin ne a rukuni biyu, tare da jagorancin daraktan yada labaran ofishin shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, inji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan
'Mu hadu a 2027': Tinubu ga yan adawa kan kwace mulkinsa, ya fadi abin da ke gabansa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori 8
Shugaba Tinubu ya yi kira ga sababbin jami’an gwamnatin da su yi aiki tukuru, su rike gaskiya da amana domin tallafa wa manufofin gwamnati na ci gaban kasa.
Sababbin sakatarorin sun haɗa da Onwusoro Ihemelandu (Abia), Ndiomu Philip (Bayelsa), Anuma Nlia (Ebonyi), Ogbodo Nnam (Enugu), da Kalba Usman (Gombe).
Vangaurd ta rahoto cewa sauran sakatarorin sun haɗa da Usman Aminu (Kebbi), Oyekunle Nwakuso (Rivers), da Nadungu Gagare (Kaduna).
Tinubu ya rantsar da kwamishinonin RMAFC
Shugaba Tinubu ya kuma rantsar da sababbin kwamishinonin RMAFC guda 21, tare da kwamishina na hukumar kwatanta wakilci da wani na hukumar kididdigar jama’a.
Kwamitin majalisar dattawa ya tabbatar da nadin kwamishinonin hukumar RMAFC a watan Agustar 2024, ciki har da Linda Oti (Abia) da Akpan Effiong (Akwa Ibom).
Sauran sun hada da Enefe Ekene (Anambra), Farfesa Steve Ugba (Benue), Cif Eyonsa (Cross River), Aruviere Egharhevwe (Delta), da Nduka Awuregu (Ebonyi).
Sauran sun haɗa da Victor Eboigbe (Edo), Wumi Ogunlola (Ekiti), Ozo Obodougo (Enugu), Kabir Mashi (Katsina da Adamu Fanda (Kano).
RMAFC ta kalubalanci gyaran harajin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar RMAFC ta ce dokokin gyaran haraji sun saba wa kundin tsarin mulki, domin sun rage mata ikon tsara rabon kudade.
RMAFC ta shawarci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da tsarin rabon VAT na hukumar don tabbatar da adalci tsakanin bangarorin gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng