Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC (jerin sunaye da mukamai)

Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC (jerin sunaye da mukamai)

A yau Juma'a 8 ga watan Fabrairu ne shugaba Muhammadu Buhari ya yi sanar da sunayen sabbin ciyamomi da kwamishinoni na Hukumar Rabon Haraji na Kasa a turance Revenue Mobilization Allocation and Fiscal Commission (RMAFC).

Fadar shugaban kasar ta bayar da wannan sanarwar ne cikin wata sako mai dauke da sa hannun hadimin shugaban kasa, Garba Shehu a yau Juma'a.

Sanarwar ta ce shugaban kasar ya mika sunayen mutane 30 din da ya nada zuwa ga majalisar dattawa domin neman amincewarsu.

Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC

Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC
Source: UGC

Ga sakon shugaban kasar a kasa:

"Kamar yadda sashi na 154(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa kwaskwarima ya tanada, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen mutane 30 da aka yiwa nadi a matsayin Ciyaman da kwamishinoni na hukumar RMAFC."

Sunayen na kunshe cikin wata wasika ne da shugaban kasar ya aike wa shugaban majalisa Bukola Saraki inda ya nemi amincewarsa cikin gaggawa.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Ga sunayen wadanda aka yiwa nadin da jihohinsu na asali:

1. Engr. Elias Mbam a matsayin Ciyaman (Ebonyi)

2. Chris Alozie Akomas a matsayin kwamishina (Abia)

3. Ayang Sunday Okon a matsayin kwamishina (Akwa Ibom)

4. Chima Philip Okafor a matsayin kwamishina (Anambra)

5. Samuel Adaa Maagbe a matsayin kwamishina (Benue)

6. Ntufam Eyo Nsa Whiley a matsayin kwamishina (Cross River)

7. Andrew Ogheneovo Agbaga a matsayin kwamishina (Delta)

8. Barr. Patrick Nworu Mgbebu a matsayin kwamishina (Ebonyi)

9. Victor Eboigbe a matsayin kwamishina (Edo)

10. Amujo Philip Ajayi a matsayin kwamishina (Ekiti)

11. Maria Chinyere Aniobi a matsayin kwamishina (Enugu)

12. Hon. Musa Tanko Abari a matsayin kwamishina (FCT)

13. Mohammed Kabeer Usman a matsayin kwamishina (Gombe)

14. Alhaji Ahmed Mahmoud Gumel a matsayin kwamishina (Jigawa)

15. Alh. Kabir Muhammad Mashi a matsayin kwamishina (Katsina)

16. Barr. Umar Farouk Abdullahi a matsayin kwamishina (Kano)

17. Rilwan Hussein Abarshi a matsayin kwamishina (Kebbi)

18. Hon. Suleiman Kokori Abdul a matsayin kwamishina (Kogi)

19. Abdullahi Shuaibu Yaman a matsayin kwamishina (Kwara)

20. Dr. Wright Olusegun Adekunle a matsayin kwamishina (Lagos)

21. Aliyu A. Abdulkadir a matsayin kwamishina (Nasarawa)

22. Ibrahim Bako Bagudu Shettima a matsayin kwamishina (Niger)

23. Fari Adebayo for a matsayin kwamishina (Ogun)

24. Tokunbo Ajasin a matsayin kwamishina ( Ondo)

25. Kolade Daniel Abimbola a matsayin kwamishina ( Oyo)

26. Alexander Shaiyen a matsayin kwamishina (Plateau)

27. Wenah Asondu Temple a matsayin kwamishina (Rivers)

28. Alhaji Modu Aji Juluri a matsayin kwamishina (Yobe)

29. Abubakar Sadiq A. Gusau a matsayin kwamishina (Zamfara)

30. Prof. Isa B. Mohammed a matsayin kwamishina (Bauchi)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel