Shettima Ya Bugi Kirji a kan Rashawa, Ya Ce za a Magance Matsalolin Najeriya

Shettima Ya Bugi Kirji a kan Rashawa, Ya Ce za a Magance Matsalolin Najeriya

  • Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana aiki tukuru wajen gyara matsalolin tattalin arziki
  • Shettima ya bayyana cewa akwai babban nauyi da ya rataya a kan wuyan shugabannin Najeriya da magance matsalolin tsaro
  • Mataimakin shugaban kasar ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa Najeriya za ta cika burinta, matasa za su zama jagororin a dimukuradiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan gwamnatin za ta ci gaba da karfafa dimukuradiyya.

Ya ce za a cimma wannan matakki ne ta hanyar gyara manyan matsalolin tattalin arziki, tsaro, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Kashim
Najeriya za ta magance rashawa Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne a birnin Abuja a ranar Litinin, yayin taron kasa kan karfafa dimukuradiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da taron da taken: “Karfafa Dimukuradiyya a Najeriya: Hanyoyin Gudanar da Gwamnati Nagari da Tsaftace Siyasa,” wanda Cibiyar Afirka ta Jagoranci, Tsare-Tsare, da Ci Gaban Al’umma ta shirya.

Shettima ya yabi tsarin dimukuradiyya

A cewar jaridar Vanguard, Shettima ya samu wakilcin Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Siyasa, Hakeem Baba-Ahmed a yayin taron.

Ya ce ko da yake dimukuradiyya ba ita ce tartibiyar hanya gudanar da shugabanci ba, amma ita ce mafi ingancin tsarin mulki idan aka kwatanta da sauran.

Ya ce:

“Ina son tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinmu tana sane da damuwar da ake nunawa kan alkiblar da muke bi da kuma manufofinmu, musamman duba da kalubalen da wasu manufofinmu ke haifarwa. Muna kan kokarin gyara matsalolin tattalin arziki da dabarun tabbatar da tsaron al’umma.

“Za mu inganta kasa,” Kashim Shettima

Kashim Shettima ya bayyana cewa shugabannin da aka zaba a Najeriya suna da babban nauyi na tallata dimukuradiyya ta hanyar ingantaccen shugabanci da tabbatar da tsaron kasa.

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

Ya kara da cewa:

“Za mu saurari jama’a, kuma mu yi gyara idan ya zama dole, kuma za mu bayar da rahoton ayyukanmu kamar yadda tsarin dimukuradiyyarmu ke bukata. Na tabbata cewa Najeriya za ta sake zama gagarumar kasa, ta cimma cikakkiyar damar da Allah ya bata.

Mataimakin Shugaban Kasar ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan da za su tabbatar da ganin Najeriya ta zama jagora a duniya.

Ya ba matasa tabbacin cewa za su yi jagoranci a dimukuradiyyar Najeriya, ganin yadda ake da bukatarsu a wajen tafiyar da kasa da ci gaban al'umma.

Shettima ya shilla kasar waje

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kashim Shettima, ya bar birnin tarayya Abuja zuwa birnin Davos na ƙasar Switzerland domin wakiltar Najeriya a taron s tattalin arziƙin na shekara-shekara.

Shettima ya halarci taron tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Jumoke Oduwole, da shugabar hukumar kula da zuba jari a Najeriya (NIPC), Aisha Rimi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.