Mutanen Katsina Sun Yi Martani, Ana Tsoron Gwamnati Ta Kinkimo Sulhu da 'Ƴan Bindiga
- An jagoranci yin sulhu da wasu shugabannin ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Wannan sulhun da aka yi da ƴan bindigan, bai yi wa wasu daga cikin mutanen ƙaramar hukumar daɗi ba, inda suka ce ko an yi ba ya aiki
- Sun nuna kuskuren gwamnatin tarayya na shirya yin sulhun ba tare da masaniyar gwamnatin jihar Katsina ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Mutanen ƙaramar hukumar Batsari da ke jihar Katsina sun yi magana kan yarjejeniyar sulhu da jami'an tsaro suka ƙulla da ƴan bindiga.
Mutanen na Batsari sun nuna rashin jin daɗinsu game da yarjejeniyar da ake cewa ƙulla kwanan nan tare da shugabannin ƴan bindiga Abu Radde, Umar Black, da sauransu a yankinsu.

Asali: Facebook
An soki yarjejeniyar sulhu da ƴan bindiga
A wata hira da jaridar Leadership, wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya soki gwamnatin tarayya kan fara wannan sulhu ba tare da sanya gwamnatin jihar Katsina a ciki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya sha nesanta kansa daga yin sulhu da ƴan ta'adda, yana mai cewa irin waɗannan yarjejeniyoyin jama'a kawai ake cuta.
Ya kuma nuna shakku kan adadin makaman da ƴan ta'addan suka miƙawa jami'an tsaro.
Sulhun wanda sojoji suka jagoranta, ya jawo shakku daga mazauna yankin, inda suka bayyana cewa zai gaza cimma nasara, ganin cewa an sha yin irinsa a baya, amma bai haifar da ɗa mai ido ba
"An taba yin irin wannan yarjejeniya da dama a baya, amma duk ba su yi tasiri ba. Wannan ma ba zai yi aiki ba."
"Gwamnatin tarayya ta yi kuskure wajen ci gaba da wannan sulhu ba tare da tuntuɓar gwamnatin jiha ba."
"Bindigogi ƙirar AK47 guda huɗu kawai daga ƙungiyar ƴan bindigan da ke da ɗaruruwan bindigogi? Wannan labari ne kawai."
- Wani mazaunin Batsari
Gwamnatin Katsina ta nesanta kanta da yin sulhu
Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Katsina, Bala Zango, ya jaddada matsayin gwamnatin jihar na ƙin shiga sulhu da ƴan ta'adda.
"Babu ruwan gwamnatin jiha a wannan yarjejeniyar sulhun. Har yanzu muna a kan matsayarmu ta duk wanda ya daina tayar hankali kuma ya miƙa makamansa, za mu yi la'akari da shi, amma ba za mu yi sulhu da ƴan ta'adda ba."
- Bala Zango
Ƴan bindiga sun kai hari a kasuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wata babbar kasuwar mako-mako da ke jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a kasuwar Ngalda sun hallaka mutane bakwai tare da raunata wasu mutane fiye da 10.
Jami'an ƴan sanda da ƴan sa-kai sun bi sahun miyagun, inda suka kashe wasu daga cikinsu, tare da cafke shugabansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng