Gwamna Ya Yi Magana kan Sulhu, Wasu Gawurtattun Yan Bindiga Sun Halarci Taro
- Gwamnatin Katsina ta musanta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, sai dai ta ce za ta karɓi waɗanda suka miƙa wuya
- An ruwaito cewa manyan gawurtattun ƴan bindiga sun halarci taron sulhu a Batsari, lamarin da gwamnatin Dikko Radda ta ce babu hannunta
- Rundunar soji ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce luguden wuta ne ya tilastawa ƴan ta'addan neman a zauna lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗda ta musanta batun shiga wata tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga.
Gwamnatin ta faɗi haka ne baya samun wasu rahotanni da suka nuna cewa an cimma yarjejeniyar zaman lafiya da wasu shugabannin ‘yan bindiga a karamar hukumar Batsari.

Asali: Facebook
Gwamna Dikko ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Dr. Bala Salisu, ya shaidawa Daily Trust ta wayar tarho cewa gwamnati Katsina na nan a kan bakarta na ba sulhu da ƴan ta'adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bala Salisu ya kuma tabbatarwa al'umma cewa babu wani zaman sulhu da gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta shiga da wasu riƙaƙƙun ƴan bindiga.
Sai dai ya jaddada cewa gwamnati a shirye take ta karɓi duk wani ɗan bindiga da ya miƙa wuya bisa ra'ayin kansa kuma ya daina aikata ta’addanci.
Gwamnati zata karɓi waɗanda suka miƙa wuya
“Ba mu shiga wata yarjejeniyar zaman lafiya ba, kuma matsayar gwamnati shi ne duk wanda ya daina aikata ta’addanci ya miƙa makamansa za a duba batunsa.
Amma ba za mu nemi tattaunawar neman sulhu da kowane ɗan bindiga ba,” in ji Dakta Salisu.
Ƴan bindiga sun nemi zaman lafiya
Rahotanni sun nuna cewa an yi wata tattaunawar zaman lafiya da ta haɗa shugabannin sojoji, wakilan DSS, sarakuna mutanen yankin a kauyen Kofa, yammacin garin Batsari.
Wani mazaunin yankin, wanda ya ce ya halarci tattaunawar ranar Lahadi, ya bayyana cewa:
“Yan bindigar sun nemi a ba su damar shiga al’umma ba tare da tsangwama ba, kuma sun yi alkawarin daina hare-haren ta'addanci.
"Sun miƙa makamansu kuma sun sako waɗanda suka yi garkuwa da su, sun yi ikirarim cewa wannan ce hanyar samun zaman lafiya.”
Gawurtattun ƴan bindiga sun halarci taron
An tattaro cewa shugabannin ‘yan bindiga kamar Lamu Saudo, Abdulhamid Dan Da, Umar Black, da Abu Radda sun miƙa makamansu tare da sako mutanen da suka yi garkuwa da su yayin taron.
Amma majiyoyin soji sun ce matsin lamba daga hare-haren dakarun sojoji ne suka sa ‘yan bindigar ba su da wani zaɓi illa su nemi zaman lafiya.
Lifutan Lawal, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 17 Brigade, ya tabbatar da wannan ci gaban, yana mai danganta shi da matsin lambar da jami’an tsaro suka yi wa ‘yan bindigar.
Harin asibitin Kankara ya fusata gwamna

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Kun ji cewa gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda ya lashi takobin hukunta masu hannu a harin da ƴan bindiga suka kai asibitin Kanƙara.
Dikko ya ce zai ƙara ɗaukar matakan tsaro ciki har da tura dakaru asibitoci domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin Katsinawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng