Abba Ya Kafawa Ganduje Tarihi da Ya Karasa Aikin da Ya Gaza a Mahaifarsa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da fitilun tituna guda 231 da titin kilomita 5 a Dawakin Tofa, garin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
- Duk da cewa an gaza kammala aikin a mulkin Ganduje, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta cika shi a matsayin daya daga cikin alkawuran yakin neman zaɓensa
- Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa ya yaba da aikin, tare da roƙon gwamnan ya sake buɗe cibiyar koyon sana'o'in da aka rufe a lokacin gwamnatin Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da fitilun tituna guda 231 da titin kilomita biyar a garin Dawakin Tofa, mahaifar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
An ruwaito cewa an gaza kammala aikin a tsawon shekaru takwas na mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Asali: Facebook
Mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya wallafa yadda aka bude aikin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta ce Abba Kabir Yusuf ya kammala aikin ne a matsayin wani bangare na alkawuran inganta rayuwar al’ummar karkara da ya yi a lokacin yakin neman zabe.
Kakakin gwamnan ya kara da cewa aiki na cikin shirye-shiryen gwamnati na samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a Kano.
Gwamna Abba ya yi aiki a mahaifar Ganduje
Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa kammala aikin titin Dawakin Tofa da fitilun tituna wani bangare ne na himmar gwamnatinsa na cika alkawuran da ya yi yayin yakin neman zaɓe.
A lokacin taron kaddamarwar, ya jaddada muhimmancin kula da sabbin kayayyakin domin guje wa lalacewa,
A karkashin haka gwamnan ya roki al’ummar garin Dawakin Tofa su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Fa'idar aikin ga al’ummar Dawakin Tofa
Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Mukhtar Bello Danmaliki, wanda mataimakinsa, Hon. Abdullahi Magaji Aliyu (Kosasshe), ya wakilta, ya yaba da aikin.
Hon. Abdullahi Magaji Aliyu ya tabbatar da cewa fitilun za su inganta tsaro da kuma harkokin kasuwanci a yankin.
Ya bayyana cewa aiki zai ba wa mazauna yankin damar samun walwala, tare da bunkasa rayuwar yau da kullum ta hanyar samar da ingantacciyar hanya da wutar lantarki.
Kiran a sake buɗe cibiyar koyon sana’o’i
Mataimakin shugaban karamar hukumar, Magaji Aliyu, ya yi kira ga gwamna Abba Kabir da ya sake buɗe cibiyar koyon sana’o’i da ke Dawakin Tofa, wadda aka rufe a lokacin mulkin Ganduje.
Ya bayyana cewa sake farfado da cibiyar zai taimaka wa matasa wajen koyon sana’o’in da za su ba su damar dogaro da kansu, tare da bunkasa tattalin arziki a yankin.
An tunawa Abba maganar kisan Hanifa
A wani rahoton, kun ji cewa an bukaci gwamnatin Kano ta sake duba maganar kisan gilla da aka yi wa wata yarinya mai suna Hanifa.
A shekarar 2022 aka kashe yarinyar kuma mai makarantarsu da aka tuhuma da laifin ya amsa kafin daga baya ya sauya magana a kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng