An Tunawa Gwamnatin Abba da Shari’ar Wanda Ya Kashe Hanifa a 2022

An Tunawa Gwamnatin Abba da Shari’ar Wanda Ya Kashe Hanifa a 2022

  • Ibrahim A Khalil ya tunatar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf da cewa bai dace a manta da batun kisan Hanifa Abubakar ba
  • AbdulMalik Tanko, malamin Hanifa ne ya amsa laifin sata da kashe yarinyar bayan ya karɓi kuɗin fansa daga hannun iyayenta
  • Injiniya Ibrahim A Khalil ya tabbatar da cewa ba za a manta da Hanifa ba, yana addu'ar Allah ya jaddada rahama a gare ta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wani mai amfani da shafin sada zumunta, Ibrahim A Khalil ya tunatar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf a kan ta waiwayi batun kisan Hanifa Abubakar.

A shekarar 2022 ne wani malamin makaranta, AbdulMalik Tanko a amsa cewa ya sace tare da kashe dalibarsa mai shekaru biyar da haihuwa.

Kara karanta wannan

Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano

Hanifa
An tunawa gwamnatin Kano kisan Hanifa Abubakar Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Legit ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun yi nasarar kama malamin, wanda ya jagoranci kai rundunar ‘yan sandan Kano har wurin da ya binne baiwar Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin kisan Hanifa Abubakar ya tayar da hankulan mazauna jihar, kuma an shafe tsawon lokaci ana buga shari’a kafin kotu ta yanke wa malamin hukuncin kisa.

An tunawa gwamnatin Kano kisan Hanifa

Ibrahim A. El-Caleel ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa bai dace gwamnatin Kano da sauran jama’a su manta da batun kisan Hanifa Abubakar ba.

Ya wallafa cewa:

“Shekaru uku da suka wuce, Abdulmalik Tanko ya amsa laifinsa na kashe yarinya mai shekaru 5, Hanifa, bayan satar ta da kuma karɓar kuɗin fansa. Saboda tsoron cewa za ta fallasa shi, ya ba ta abin sha mai shinkafar bera. Ta rasu, sannan ya binne ta a kabari. Ita ce ɗaya tilo da iyayenta su ka haifa.
"Jami'an 'Yan Sanda na Najeriya sunyi bincike na ƙwarai, suka kuma kama shi. A ƙarshe, an shigar da shi kotu, inda kotu mai iko ta same shi da laifi, ta yanke masa hukuncin kisa a shekarar 2023."

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

An nemi bahasin mantawa da malamin Hanifa

El-Caleel ya jero wasu tambayoyi da ke neman sanin dalilin da ya sa aka jinkirta zartar da hukuncin kisa da kotu ta zartar a kan AbdulMalik Tanko.

Ya ce;

“Me gwamnati ta ke jira? Me yasa al'umma ke shiru yayin da shari'a ke tafiyar hawainiya a kowace rana? Me yasa muke jin daɗi da wannan? Wannan mai kisan zai iya kashe ɗaya daga cikin yaran ku da kuka tura masa don koyar da su.”
“Ba za mu manta da Hanifa ba. Allah ya dawwamar da ita a cikin rahama a Al-Jannatul Firdaws. Allah ya ba iyayenta haƙuri da juriya. Ameen.”
“Ba za mu manta ba”

Makashin Hanifa ya daukaka kara

A baya, mun ruwaito cewa AbdulMalik Tanko da abokinsa, Hashimu Isyaku sun daukaka kara su na neman a janye hukuncin kisa da wata kotu a Kano ta yanke masu saboda laifin kashe Hanifa Abubakar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Lauyansu, Anthony Ezenwoko, ya kalubalanci shaidun da aka gabatar a gaban kotu, yana mai cewa ba su tabbatar da laifin da ake zarginsu da aikatawa ba, inda ya ce an yanke hukunci bisa kuskure.

Tun da fari, an gurfanar da AbdulMalik Tanko a gaban kotu bayan gano cewa ya na da hannu a cikin satar dalibarsa Hanifa tare da hadin bakin wasu mutane guda biyu, sannan ya hallaka ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.