Shugaba Tinubu Ya Kafa Sabuwar Makarantar Kimiyya da Fasaha, Ya Raɗa Mata Sunansa
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha a Gwarinpa, ɗaya daga cikin manyan unguwanni a Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa za a raɗawa sabuwar makaranta sunan Bola Tinubu domin girmamama mai girma shugaban ƙasa
- Shugaban ƙaramar hukumar kwaryar birni watau AMAC ya yabawa Shugaba Tinubu bisa cika burin da suka daɗe suna mafarkinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a Gwarinpa, daya daga cikin manyan unguwannin Abuja, babban birnin kasar.
An ruwaito cewa wannan sabuwar makaranta za a sanya mata suna 'Bola Ahmed Tinubu Polytechnic' domin karrama mai girma shugaban kasa.

Asali: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa hakan na ƙunshe a wata wasika mai kwanan wata 16 ga Janairu, 2025, da aka aike wa ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya kafa sabuwar makaranta
Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da kafa wannan kwalejin a Gwarinpa domin inganta horon fasaha, sana’o’i da dabarun kasuwanci bisa tsarin dokar ilimi ta kasa.
A cikin wasikar wadda Dakta Alausa ya sa hannu da kansa, ya nemi Wike ya bayar da shawarim wuraren da za a kafa makarantar na wucin gadi da na dindindin a Gwarinpa domin fara aiki.
Ministan ya kara da cewa kwararru daga ma’aikatar ilimi da hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) za su ziyarci wuraren da aka bada shawarar domin duba su.
A cewarsa, bayan haka ne gwamnati za ta ɗauki matsaya kan wurin da za a gina makaranta bisa rahoton da tawagar za ta gabatar.
Shugaban AMAC ya yabawa Bola Tinubu
A nasa ɓangaren, shugaban karamar hukumar kwaryar birnin Abuja (AMAC), Christopher Zakka Maikalangu, ya yaba wa shugaba Tinubu bisa amincewa da kafa kwalejin a Gwarinpa.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da al’amuran jama’a, Kingsley Madaki, ya fitar, Maikalangu ya nuna godewa ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ya ce dole ne ya godewa Wike saboda rawar da ya taka wajen ganin wannan mafarkin ya zama gaskiya ga mazauna Abuja.
Maikalangu ya bayyana kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Gwarinpa a matsayin buri da ya zama gaskiya, wanda zai taimaka wajen kawo ci gaba ga mazauna birnin.
Tinubu ya fara ba ɗan Abuja minista a tarihi
Ya kuma ƙara da cewa a karon farko a tarihin kasar, wani ɗan asalin Abuja, Zaphaniah Bitrus Jisalo, ya zama minista a Najeriya.
Shugaban AMAC ya ce Bitrus Jisalo ɗan asalin Abuja ne kuma ya wakilci mazabar AMAC/Bwari a Majalisar wakilan tarayya na tsawon zango biyu.
Mace ta zama mataimakiyar shugaban DSS
A wani labarin, kun ji cewa mai girma shugaban ƙasa ya naɗa mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban hukumar DSS ta ƙasa.
Ma'aikatan hukumar ƴan sandan farin kaya da aka fi sani da DSS na yanzu da waɗanda suka riga suka ajiye aiki sun yaba da naɗin Folashade Arinola.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng