NCC Ta Amince da Ƙarin Kudin Kira, MTN, Airtel da Glo ba Su Samu Yadda Suke So ba
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar sadarwa ta ƙasa watau NCC ta amince kamfanonin sadarwa su ƙara kudin kira da kaso 50%
- Mai magana da yawun NCC, Reuben Mouka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 20 ga watan Janairu, 2025
- Tun farko kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel da Glo sun bukaci a ba su dama su nunka kuɗim kiran waya, lamarin da NCC ta ce ya yi yawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da buƙatar MTN, Airtel, Glo da sauran kamfanonin sadarwa na ƙara kudin kira.
Mai magana da yawun NCC na ƙasa, Reuben Mouka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 20 ga watan Janairu, 2024.

Asali: Twitter
A sanarwar da NCC ta wallafa a shafin X, Mouka ya ce hukumar ta amince da ƙarin ne dogaro da sashi na 108 na dokar sadarwa 2003 (NCA).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dokar ta bai wa hukumar NCC ƙarfin ikon sa ido da amincewa da tsarin kudin kira, sayen data da tura saƙonni na kowane kamfanin sadarwa.
Hukumar NCC ta amince da ƙarin kaso 50%
Mouka ya ce kamfanonin sadarwa sun bukaci yin ƙarin ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da kuma yanayin kasuwa a yanzu.
"Ƙarin ba zai haura kaso 50% daga tsarin kuɗin kiran yanzu ba, duk da bai kai 100% da galibin kamfanonin suka nema ba, an tsara karin ne duba da gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren sadarwa."
"Wannan ƙarin zai kasance bisa dokokin da NCC ta gindaya kuma za a duba kowace bukata da kamfanonin sadarwar suka gabatar.
"Tun 2013 ba a ƙara yin ƙarin kudin sadarwa ba duk da tsadar kayan aiki da kamfanonin sadarwa ke fuskanta, don haka an yi wannan kari ne don daidaita farashin aiki da kudin sadarwa."
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan ƙarin zai taimaka wajen inganta ayyukan sadarwa da kuma samar da sabis mai ƙarfi ga ƴan Najeriya.
NCC ta san halin tsadar da ake ciki a Najeriya
Mouka ya kara da cewa, NCC ta fahimci bukatar samar da daidaito tsakanin kare masu amfani da layukan sadarwa da kuma tabbatar da dorewar masana’antar.
"Hukumar NCC ta san halin da magidanta da ƴan kasuwa ke fuskanta a ƙaar nan kuma ta damu matuƙar da tasirin da ƙarin kudin sadarwa zai yi wa mutane.
"Don haka ne ma muka umarci kamfanonin sadarwa su yi wannan ƙari a bayyane kuma ta hanyar da ta dace ba tare da cutar da kwastomomi ba.
"Akwai buƙatar kamfanonin su ilimantar tare da wayar da kan jama'a kan sabon ƙarin da suka da kuma ƙoƙarin samar da sabis mai inganci," in ji shi.
Gwamnatin Tarayya ta gana da kamfanoni
A wani labarin, kun ji cewa ministan sadarwa, Bosun Tijani ya yi wata ganawa da wakilan kamfanonin sadarwa kan batun ƙarin kudin kira.
Taron ya samu wakiltar manyan masu ruwa da tsaki a ɓangaren harkokin sadarwa da kuma hukumomin gwamnati masu alhakin kula da lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng