Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani game da Shirin Karin Kudin Kira da Sayen Data
A makon jiya ne gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin sanarwa su yi ƙarin kuɗin kiran waya, sayen data da tura sakon SMS a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gwamnatin ta amince da buƙatar kamfanonin sadarwar ne bayan shafe sa'o'i suna tattaunawa kan lamarin a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ministan sadarwa, kirƙire-kirkire da tattalin arzikin zamani Bosun Tijani ya ce za a yi karin kuɗin kira amma ba za a nunka ba.
Tun farko dai kamfanonin sadarwa irinsu MTN da Airtel sun nemi gwamnatin Najeriya ta sahale masu su kara kuɗin kiran waya saboda tsadar kayayyaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanonin sun gabatar da buƙatar ƙarin kaso 100% watau nunka kuɗin kira da sayen data ga ƴan Najeriya, lamarin da gwamnati ta ce ba ta yarda ba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku abubuwan da ya kamata ku sani game da shirin ƙarin kuɗin sadarwa da za a yi nan kusa a Najeriya.
Shirin ƙarin kuɗin sadarwa a Najeriya
Kamfanonin sadarwa da ke aiki a Najeriya irinsu MTN, Airtel, Glo, 9Mobile da sauransu sun matsa cewa dole su ƙara kuɗi idan har ana son sabis mai ƙarfi da inganci.
Wannan mataki da suke shirin ɗauka zai shafi kiran waya, sayen data da kuma tura saƙonnin SMS ga masu amfani da layukan sadarwa a ƙasar nan.
Ƙarin kuɗin da za a yi ya samo asali ne daga tsadar rayuwar da ake ciki wanda su kansu kamfanonin suka koka kan hauhawar kayan aikinsu.
Meyasa kamfanoni suka matsa kan ƙarin?
Tun farko dai kamfanonin sadarwa sun matsawa gwamnatin Najeriya cewa ya kamata ta amince su ƙara kuɗin harkokin sadarwa duba da halin da ake ciki.
A wani rahoto da Arise TV ta wallafa, shugaban kamfanin MTN, Karl Toriola, ya ce za su kara kudin kiran waya da 100% da zarar hukumar kula da sadarwa (NCC) ta ba su damar yin hakan.
Har ila yau, shugaban ƙungiyar kamfanonin sadarwa watau ALTON, Injiniya Gbenga Adebayo ya ce ba za su iya ci gaba da aiki a haka ba domin babu wata riba.
Ya ce hauhawar farashin kayan aiki, karuwar kudin wutar lantarki, tsadar dala da hauhawar farashi sun haifar da babban matsin tattalin arziki ga kamfanonin.
A cewarsa, kamfanonin ba za su iya ci gaba da kula da layukan sabis da inganta su ba matuƙar ba a ba su damar yin ƙarin kudin sadarwa ba.
Manyan abubuwan da suka fi kokawa a kai su ne tsadar man dizel, tashin farashin kayayyaki, da ƙarin haraji wanda suka ce ya rage ribar da suke samu.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Me zai sauya idan aka yi karin?
Duk wasu harkokin sadarwa da ake yi da layukan MTN, Airtel da sauran lauyukan kamfanoni zai tashi da zaran an ƙarkare adadin ƙarin da za a yi.
Kuɗin da ake kashewa wajen kiran waya zai ƙaru da zarar an yi wannan kari da ake ta magana a kai.
Amfani da intanet, kallon bidiyo, da amfani da kafofin sada zumunta na iya zama mafi tsada saboda kuɗin sayen data zai ƙaru.
Haka nan kuma kudin tura sakon SMS zai karu duk da cewaɓa yanzu an daina yawan tura saƙonni saboda kafafen sada zumunta.
Yadda ƙarin kudin kira zai shafi ƴan Najeriya
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya watau NCC ta tabbatar da cewa ba za ta bari a yi ƙarin da zai kara matsawa ƴan Najeriya ba.
To sai dai duk da haka ƙarin ba zai yi wa mutane daɗi ba duba da halin ƙunci da tsadar rayuwar da ake ciki, galibi magidanta sun fi bai wa abinci fifiko.
Wannan kari ka iya ƙara tsanantawa ƴan Najeriya musamman masu kananan sana'o'i waɗanda ke amfani da sabis na kamfanonin sadarwa.
Wani mai shagon intanet watau Cafe, Sama'ila Isah ya shaidawa Legit Hausa cewa dole ne za su ƙara kudin aikinsu idan har kudin sayen data ya ƙaru.
"Duk a kan talaka zai kare, mu kanmu idan aka kara kuɗin data ya zama dole mu ƙara kudin aiki, Allah ya kawo mana sauƙi," in ji shi.
Menene mataki na gaba?
NCC da kamfanonin sadarwa za su ci gaba da tattaunawa don tabbatar da cewa karin kudin ya dace da yanayin tattalin arziki da ci gaban ɓangaren sadarwa.
A wata hira da ya yi da Channels tv cikin shirin siyasa a yau, Ministan sadarwa ya ce ƙarin kudin kiran da za a yi ba zai wuce kashi 30% zuwa 60% ba.
Da yake jaddada bukatar dorewar fannin sadarwa daidai da ƙarfin ‘yan Najeriya, ya ce, “Ina ganin bai kamata ya wuce kashi 30% zuwa 60% ba.”
A rahoton Bussiness Day, Bosun Tijjani ya ce fannin sadarwa yana ba da gudummuwa ga tattalin arzikin ƙasa kuma yana rage marasa aikin yi a ƙasa.
Duk da cewa karin kudin na iya kawo ƙalubale, za a yi shi ne don tallafa wa masana’antar sadarwa ta ci gaba da samar da sabis mai inganci ga ‘yan Najeriya.
Ministan Tinubu ya gana da kamfanonin sadarwa
A wani labarin, kun ji cewa ministan sadarwa. Bosun Tijani ya gana da wakilan MTN, Airtel da sauran kamfanonin sadarwa kan batun karin kudin kira.
Manyan masu ruwa da tsaki da hukumomin lamarin ya shafa sun halarci zaman wanda ya maida hankali kan buƙatar kara kudin sadarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng