Karin Kudin Kira: Farfesa Pantami Ya Fadi Yadda Barinsa Ofis Ya Yi wa Wasu Dadi

Karin Kudin Kira: Farfesa Pantami Ya Fadi Yadda Barinsa Ofis Ya Yi wa Wasu Dadi

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana dalilinsa na kin amincewa da bukatar kamfanonin sadarwa na kara farashin kira
  • Ya ce a lokacin ya na Minista, akwai mutanen da kamfanonin da ke lallaba wa domin samun amincewar gwamnati don yin karin
  • Wannan batu ya kara bayyana a kafafen sada zumunta bayan gwamnatin Bola Ahhmed Tinubu ta amince da karin kudin kira da 50%

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - 'Yan Najeriya sun fara waiwaye a kan yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsaya kai da fata wajen hana karin kudin kira, tare da karo kudin shiga ga gwamnati.

Farfesa Isa Ali Pantami, wanda shi ne tsohon Ministan sadarwa na kasa, Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda ya ki amincewa da bukatar kamfanonin.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Pantami
Gwamnatin Buhari ba ta amince da karin kudin kira ba Hoto: Prof Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

A wani tuna baya da Abdullahi Giggs ya wallafa a shafinsa na Facebook, Farfesa Pantami ya bayyana cewa ya samu kudin 1G na data a kan N1,200, amma farashi ya karye daga baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kara wallafa bidiyon ne a lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ta amince da karin 50% na kudin kira da data ga 'yan Najeriya.

'An samu karin kudin shiga," Farfesa Pantami

Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa an yi nasarar samun karin kudin shiga a ma'aikatarsa ba tare da an kara farashin kudin kira ko takurawa talakawa ba.

Ya bayyawa cewa;

"Kar ku manta, tunda na shiga ofis ba a taba kara kudin buga waya ko data na kwana daya ba. Zuwan da na yi, 1G na data, ana sayensa a kan N1200 ne. Bayan na kammala na fita ya koma N320."

Yadda Farfesa Pantami ya inganta sabis a Najeriya

Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa an yi tsayin daka a zamaninsa wajen tabbatar da cewa an samu ingancin sabis na waya da data.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Ya ce ya sha wahala sosai a lokacin, wanda ya biyo bayan bukatar sa ido da tabbatar da cewa 'yan Najeriya ba su fuskanci wani kalubalen network ba.

Farfesa Pantami ya kara da cewa;

"A lokacin ko mutum daya na gani a Facebook ko twitter (X) ya yi korafi sai na sa an kira dukkanin kamfanonin waya, in network ya yi kasa, ba na bacci sai ya gyaru a Najeriya, don ina tsoron kar na mutu Allah ya tambaye ni."

Pantami ya fadi yadda ake shugabanci

Fitaccen malamin addinin musulunci kuma tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya dace shugabanni su tafiyar da mabiyansu.

Ya ce;

"In mutum ya san shugabanci, babban aikin shugaba, shi ne tausaya wa rayuwar talakawa. Duk matakin da za ka dauka, idan talaka zai wahala, kar ka yi shi. Duk abin da zai sa talaka ya tozarta kar a yi shi."

"An ji dadi na bar ofis," Pantami

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya yi wankin babban bargo ga Wike kan Tinubu

Shekih Isa Ali Pantami ya bayyana cewa wasu manyan kamfanonin sadarwa sun bayyana masa bukatarsu na neman amincewar gwamnati don karin farashin kudin kira.

Ya ce a lokacin da wa'adinsa ya kare, an samu wadanda su ka yi bakin ciki, tare da farin ciki a lokaci guda saboda za su samu damar kara farashin kira.

Farfesa Pantami ya magantu kan fito wa takara

A baya, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami, ya yi bayani a kan bukatar 'Gombe State Promoters Forum in Broadcasting Media'.

Farfesa Pantami ya gode wa ƙungiyar bisa kiran da suka yi masa na ya fito takara, tare da bayyana cewa zai sanar da masoyansa shawarar da ya yanke kafin zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.