Izala Ta yi Magana kan Zargin Hada Alarammomi a Goyi Bayan Tinubu a 2027

Izala Ta yi Magana kan Zargin Hada Alarammomi a Goyi Bayan Tinubu a 2027

  • Sheikh Ibrahim Idris ya yi karin haske kan zargin da ake yi cewa za a yi amfani da taron Qur'anic Festival domin tallata Bola Tinubu a 2027
  • Malamin ya bayyana cewa taron ba na Izala ba ne, Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ce ke shirya shi
  • Ya yi gargadi ga masu siyasantar da taron tare da tabbatar da cewa manufarsa ita ce inganta koyarwa da haddar Alkur’ani mai girma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Daya daga cikin malaman kungiyar Izala, Sheikh Dr Ibrahim Idris ya yi karin haske kan taron ‘Qur’anic Festival’ da ake shirin gudanarwa a Najeriya.

Malamin ya yi bayanin ne yayin da ake rade-radin cewa za a tara mahaddata Qur'ani 30,000 domin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

Kungiyar Izala
Izala ta warware zargin hada mahaddata Kur'ani da manufar siyasa. Hoto: Jibwis Nigeria|Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation
Asali: Facebook

A wani bidiyo da shafin Jibwis Najeriya ya wallafa a Facebook, malamin ya ce taron ba na kungiyar Izala ba ne, Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci ce ta shirya shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin jawabi, Sheikh Dr Ibrahim Idris ya yi kira ga masu suka da su bincika gaskiyar al’amari kafin yin furuci kan batutuwan da suka shafi addini da siyasa.

Matsayar Izala kan taron Qur'anic Festival

Sheikh Idris ya yi karin haske cewa taron Qur'anic Festival ba shi da alaka kai tsaye da kungiyar Izala.

Ya bayyana cewa;

“Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ce ta shirya taron, ba Izala ba. Taron zai samu halartar manyan malamai kamar Farfesa Mansur Sokoto da Dr Bashir Aliyu Umar.”

Malamin ya jaddada cewa wasu suna zargin Izala da kokarin rusa tsarin koyarwa da haddar Alkur’ani a Najeriya, amma wannan zargi ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Ya kara da cewa wannan taro na da nufin bunkasa haddar Alkur’ani da samar da dabarun koyarwa da karatun Alkur’ani a Najeriya da ma duniya baki daya.

Manufofin taron Qur'anic Festival

Dr Ibrahim Idris ya bayyana cewa daga cikin manufofin taron akwai:

  • Samar da hanyoyin koyon haddar Alkur’ani mai girma a fadin duniya.
  • Koyar da masu bukata ta musamman karatun Alkur’ani.
  • Yin bayani kan hikimomi wajen karatu da karantar da Alkur’ani.

Ya ce cikin malaman da suka yi na'am da taron akwai Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara.

A cewar malamin, haduwar malamai a taron ba matsala ba ce domin manufar taron ba ta shafi akida ko siyasa ba.

Gargadi ga masu siyasantar da taron

A martaninsa kan masu ikirarin cewa za a yi amfani da taron domin tallata Tinubu a 2027, Sheikh Idris ya gargadi masu irin wannan tunani.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

“Taron ba domin siyasa ba ne, kuma mutane su jira a ga abin da za a tattauna kafin yanke hukunci,”

Wanene ya dauki nauyin taron Quranic Festival?

Malamin ya yi martani ga masu ikirarin cewa gwamnatin tarayya ce za ta dauki nauyin shirin da maganganu masu kama da haka.

Ya bayyana cewa ko da gwamnati ta lalace, ba za a iya yanke alaka da ita ba saboda bukatar hada kai wajen warware matsalolin al’umma.

Almajiranci da burin kawo gyara

Daga cikin manufofin taron, Sheikh Idris ya bayyana cewa akwai samar da mafita ga matsalolin da suka shafi almajiranci a Najeriya.

Ya ce wasu daga cikin masu sukar tsarin almajiranci na daga cikin masu sukar taron, amma ya kamata su gane cewa manufar taron ita ce warware irin wadannan matsalolin.

Auwal Yusuf Sambo Rigachukun ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa malaman Izala sun yi jimamin rasuwar babban dan mataimakin shugaban majalisar malaman kungiyar, Auwal Yusuf Sambo.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo na cikin malamin da suka yi ta'aziyya ga Sheikh Yusufu Muhammad Sambo Rigachikun kan rashin da aka masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng