Jagororin Izala Sun Yi Jimamin Rasuwar Auwal Yusuf Sambo Rigachikun

Jagororin Izala Sun Yi Jimamin Rasuwar Auwal Yusuf Sambo Rigachikun

  • Sheikh Yusufu Muhammad Sambo Rigachikun ya sanar da rasuwar dansa, Auwal Yusuf Sambo, tare da lokacin masa jana’iza a Kaduna
  • Manyan malaman addini, ciki har da Sheikh Ahmad Gumi da Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo, sun yi ta’aziyya ga iyalan marigayin
  • Mabiya kungiyar Izala sun yi addu’a da rokon Allah ya gafarta wa marigayin tare da bai wa iyalansa juriyar wannan babban rashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - A ranar Litinin, 20 ga watan Janairu, 2025, za a gudanar da jana’izar Auwal Yusuf Sambo, babban ɗan Sheikh Yusufu Muhammad Sambo Rigachikun.

Malaman addini da shugabannin kungiyar Izala sun yi ta’aziyya tare da yin addu’a ga marigayin suna cewa rashin ya bar babban gibi a cikin iyalansa da al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Yusuf Sambo
An sanar da rasuwar Auwal Yusuf Sambo. Hoto: Saleem Yusuf Muhammad Sambo
Asali: Facebook

Sheikh Yusufu Muhammad Sambo Rigachikun da kanasa ya wallafa labarin rasuwar dan nasa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar rasuwar Auwal Yusuf Sambo

Mataimakin shugaban malaman Izalar Jos, Sheikh Yusufu Muhammad Sambo Rigachikun ya sanar da rasuwar dansa, Auwal Yusuf Sambo.

Malamin ya bayyana cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a kofar gidansa da ke Rigachikun, Kaduna, da misalin ƙarfe 10:30 na safe.

A cikin sanarwar da ya fitar, Sheikh Yusufu Sambo Rigachikun ya ce:

“Allah ya jikansa, ya gafarta masa, ya sanya Aljanna ce makomarsa,”

Ta’aziyyar Auwal Yusuf Sambo

Shahararren malamin addinin Musulunci, Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin tare da addu’ar Allah ya gafarta wa Auwal Yusuf Sambo.

Sheikh Ahmad Gumi ya kuma bayyana alhinin sa bisa wannan babban rashin a shafinsa na Facebook jim kadan bayan sanar da rasuwar.

Shugaban majalisar malaman Izala, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi ta’aziyya a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta:

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya jajanta da Malamin Musulunci, yayan gwamna suka kwanta dama

“Allah ya gafarta wa Ustaz Auwal Yusufu Muhammad Sambo Rigachikun: Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya ba shi Aljannar Firdausi.”

Jimamin jagorori da mabiyan Izala

Jagororin kungiyar Izala da mabiya sun bayyana alhininsu tare da nuna juyayi kan rasuwar Auwal Yusuf Sambo.

Sun yi addu’a ga Allah ya gafarta wa marigayin tare da bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashi.

Mabiya sun kuma bayyana godiyarsu ga irin jajircewar Sheikh Yusufu Sambo wajen wa’azi da shugabantar al’umma, wanda hakan ya sanya ake ganin wannan rashin a matsayin babban gibi.

Kira ga jama’a su halarci jana’iza

An yi kira ga jama’a su halarci jana’izar Auwal Yusuf Sambo domin nuna alhini da addu’a ga marigayin.

Ana ganin rashin a matsayin babban darasi ne ga al’umma wajen tunawa da muhimmancin tsarkake zuciya da addu’a domin samun rahamar Allah a ranar ƙarshe.

Kano: Shirin Hisbah a shekarar 2025

Kara karanta wannan

Ganduje ya sabunta katafaren masallaci, malamai da 'yan siyasa sun hallara

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar Hisbah a jihar Kano ta bayyana shirin cigaba da ayyukan alheri a jihar Kano a 2025.

An ruwaito cewa mataimakin shugaban Hisbah na jihar Kano ne ya yi jawabin yayin da yake bayyana manyan nasarorin da suka samu a 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng