Mambilla: Bayan Buhari da Obasanjo, Lambar Shugaban Kamfanin Sunrise Ya Fito a Kotun Duniya
- Shugaban kamfanin Sunrise Power, Leno Adesanya, zai bayyana a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) a Paris yau a shari'arsa da gwamnati
- Kamfanin, ta hannun lauyansa, Femi Falana SAN ya shigar da kara domin neman gwamnatin Najeriya ta biya shi Dala biliyan 2.3 saboda wasu dalilai
- Kamfanin Sunrise ya fara shari’a da gwamnati a 2017, yana neman diyya saboda zargin karya yarjejeniya a aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban kamfanin Sunrise Power, Leno Adesanya, zai bayyana a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) a birnin Paris, kasar Faransa, yau, domin bayar da shaida a kan Najeriya.
Za a saurari shaidar Adesanya ne kan shari’ar $2.3bn da kamfaninsa ya shigar a gaban kotun, yana zargin gwamnatin Najeriya da karya yarjejeniyar da aka kulla.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust sun nuna cewa tsoffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari za su kuma bayar da shaida a gaban kotun ta ICC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 10 ga Oktoba, 2017, kamfanin Sunrise ya fara shari’ar kotun sasantawa a ICC, Paris, yana neman a biya shi diyyar $2.354bn saboda zargin karya yarjejeniyar aiki.
Asalin sabanin kamfanin Sunrise da gwamnati
Trust Radio ta bayyana cewa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, a 2017, ya bayyana Sunrise Power a matsayin "mai shiga tsakani."
Ya ce gwamnatin Buhari ta sanya hannu da kamfanin Sinohydro Corporation Limited, wani kamfani na kasar Sin, wanda ke gudanar da aikin gina tashar wutar lantarki ta Mambilla.
Aikin, wanda aka kulla yarjejeniya a 2003 zai samar da tashar wutar mai karfin megawatt 3,050 a Mambilla, jihar Taraba a kan Dala biliyan 6.
Kamfanin Sunrise ya maka gwamnati a kotu

Kara karanta wannan
Bayan kokarin titsiye shi kan badakalar $2.3bn na kwangila, Buhari ya dawo Najeriya
Bayan doguwar tattaunawa, tsohon Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, ya ce an cimma matsaya ta domin sasantawa a wajen kotu inda gwamnati ta amince da biyan $200m.
Sai dai, Sunrise ta sake shigar da kara a kotun ICC, tana neman diyya ta $400m saboda zargin karya yarjejeniyar sabuwar sulhu da aka cimma a baya.
Kamfanin ya ce gwamnatin ta kasa biyan kudin sulhun cikin kwanaki 14 kamar yadda aka sanya hannu a yarjejeniyar da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Sale Mamman suka wakilta gwamnati.
Lauyan kamfanin, Femi Falana, ya shigar da kara a Kotun Sasanta Rikicin Kasuwanci ta Duniya a ranar 11 ga Mayu, yana neman $400m a matsayin diyya.
Gwamnati ta koka a kan hauhawar farashi
A baya, kun ji cewa Ministan kudi da tsara tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na iya bakin kokarinta wajen dawo da tattalin arziki hayyacinsa.

Kara karanta wannan
"A bar mu da talaucinmu": Shettima ya fadi matsayarsa kan dogara da tallafin turawa
A lokacin da ya bayyana a gaban majalisa domin kare kasafin kudin ma'aikatarsa, Mista Edun ya ce amma akwai babbar matsala da ke ci gaba da kawo cikas wajen dakile kokarin da ake yi.
Sai dai majalisa ta shaidawa Ministan cewa akwai bukatar gwamnati ta sake duba matsalar hauhawar farashi da yadda ta yi hasashensa a kasafin kudin 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng