Take doka: Jami'an tsaro sun damke Yusuf Sambo Rigachukun da dansa

Take doka: Jami'an tsaro sun damke Yusuf Sambo Rigachukun da dansa

Babban hafsin soja mai mukamin Janar ya shiga hannun 'yan sanda a jihar Kaduna sakamakon karya dokar hana zirga-zirga.

A wata takarda da ta fita a ranar Litinin, Aisha Dikko, kwamishinar shari'a ta jihar Kaduna, ta ce janar din sojan ya shiga hannu ne bayan yana sanye da cikakkun kayan aikinsa yayin da yake tuki daga Abuja.

Ya kasance tare da wasu fasinjoji uku wadanda basu saka takunkumin fuska ba.

Take doka: Jami'an tsaro sun damke Yusuf Sambo Rigachukun da dansa

Take doka: Jami'an tsaro sun damke Yusuf Sambo Rigachukun da dansa Hoto: Africa Prime News
Source: UGC

"Janar din ya bayyana ko shi waye kuma ya tabbatar da cewa yana tahowa daga Abuja ne a kan wani aiki na musamman da zai yi," kwamishinar tace.

"Amma kuma, kotun ta hukunta shi tare da sauran fasinjojin uku a kan take dokar zaman gida da kuma rashin saka takunkumin fuska."

Ta kara da cewa, jami'an tsaro sun damke babban malami Yusuf Sambo Rigachukun da dansa sakamakon take dokar.

Ta ce an kama malamin da dansa ne a shataletalen jami'ar jihar Kaduna a ranar Talata ba tare da takunkumin fuska ba.

Kwamishinan ya ce, malamin ya sanar da kotun cewa ya bar gida ne saboda amsa gayyatar da aka yi masa a gidan rediyon jihar Kaduna.

"An ci tarar Rigachukun da dansa saboda basu saka takunkumin fuska ba. Kowannensu ya biya N5000," tace.

Hakazalika, kotun ta bukaci malamin da ya hidimtawa al'umma ta hanyar wayar musu da kai a kan yadda za su gujewa yada annobar Coronavirus.

Kwamishinan ta kara da cewa, mutum 75 daga cikin 105 aka hukunta sakamakon zargin su da ake da take dokar hana shiga wata jiha.

KU KARATA KUMA: Kano: Shugaban majalisar limamai, Falalu Dan Almajiri, ya rasu

Dikko ta ja kunnen mazauna jihar da su kiyaye take doka don za a ci tararsu kuma a sa su aikin hidimtawa yankinsu na kwanaki bakwai.

A gefe guda, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa al’ummar jahar Kano daman gudanar da sallolin Juma’a tare da sallar Idi, duk da dokar zaman gida da gwamnatin tarayya ta sanya.

Babban mashawarcin gwamnan a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel