Banbancin ra'ayi: Wani Jigo a Izala ya ce shi Atiku zai zaba a 2019

Banbancin ra'ayi: Wani Jigo a Izala ya ce shi Atiku zai zaba a 2019

- Fittaccen malamin Izala da ke garin Kaduna, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce shi Atiku Abubakar zai zaba a zaben 2019

- Wannan matsayar nasa ya sha banban da matsayar da shugabanin kungiyar na kasa suka cimma ba na goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari

- Sheikh Sambo Rigachikun ya ce zai zabi Atiku ne saboda shine dan takarar da ya fi yiwa addinin musulunci hidima tare da taimakon 'yan kasa

Babban malamin addinin musulunci kuma jigo a kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah, (JIBWIS) Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce dan takarar shugabancin kasa na PDP Atiku Abubakar zai jefawa kuri'a a zaben 2019.

A kwana kwanan nan ne shugabanin kungiyar Izala na kasa suka bukaci 'ya'yan jam'iyyar su zabi dan takarar jam'iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari a yunkurinsa na neman zarcewa karo na biyu.

Banbancin ra'ayi: Wani Jigo a Izala ya ce shi Atiku zai zaba a 2019
Banbancin ra'ayi: Wani Jigo a Izala ya ce shi Atiku zai zaba a 2019
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: Ku zabi Buhari, kungiyar Izala ta umurci 'ya'yanta

A hirar da ya yi da wakilin BBC, Mustapha Kaita, Sheikh Sambo ya fadi dalilin da yasa zai zabi Atiku Abubakar.

"Zan zabi dan takarar da yafi taimakon addinin Musulunci da taimakon al'ummar kasa da amfanar da sum," a cewar Sheikh Sambo.

Babban malamin ya yi ikirarin cewa ya kwashe shekara 30 da sanin Atiku kuma ya ce Atikun ya gina masallatan Juma'a fiye da 100.

Wannan ra'ayin nasa ya sha banban da na shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da ya ce kungiyar ta cimma matsayar zaben Buhari ne bayan wani taro da suka gudanar.

Shugaban masu da'awah na kungiyar, Ibrahim Jalo-Jalingo ya ce kungiyar ta cimma matsayan goyon bayan Buhari ne saboda nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fanin yaki da rashawa, yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, farfado da noma da tattalin arzikin Najeriya.

"Al'umma sunyi na'am da nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu cikin shekaru uku da rabi hakan yasa muka yanke shawarar fadawa mambobin mu su zabi Shugaba Muhammadu Buhari da sauran 'yan takarar da ke aiki tare da shi," inji shi.

A cewar babban malamin, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana kan alkibla shi yasa kungiyar Izala ke goyon bayan ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel