'Ku bar Wadaƙa da Dukiyar Al'umma': Sanatan APC ga Gwamnonin Arewa kan Haraji

'Ku bar Wadaƙa da Dukiyar Al'umma': Sanatan APC ga Gwamnonin Arewa kan Haraji

  • Sanata Orji Kalu ya bukaci gwamnoni su rage kashe kudade kan motoci masu tsada, su mai da hankali kan jan hankalin masu zuba jari domin bunkasa tattalin arziki
  • A cewarsa, kowace jiha a Najeriya na da damar samun dogaro da kai idan gwamnoni suka fi mayar da hankali kan bunkasa arzikin jihohinsu
  • Kalu ya yi kira ga gwamnoni su mai da hankali kan amfani da albarkatun da Allah ya ba kowace jiha don samar da ayyukan yi da arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Umuahia, Abia - Sanata Orji Kalu ya shawarci gwamnoni su daina kashe kudade wajen siyan motocin alfarma domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Sanatan ya bukaci gwamnonin su mayar da hankali kan jan hankalin masu zuba jari domin samun kudin shiga.

Sanata ya ba gwamnonin Arewa shawara kan kudirin haraji
Sanata Orji Uzor Kalu ya shawarci gwamnoni su manta da batun siyan motocin alfarma domin inganta jihohinsu. Hoto: Senator Orji Uzor Kalu.
Asali: Facebook

Gwamnoni sun samu matsaya kan kudirin haraji

Kara karanta wannan

Rikicin Tinubu da gwamnan Bauchi: Minista ya fadi dalilin rashin jituwa

A wata hira da Arise TV, Kalu ya ce gwamnatocin jihohi su daina dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya, su yi amfani da albarkatun jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganganun Kalu sun biyo bayan matsayar gwamnonin Najeriya game da tsarin raba kudin VAT, musamman ga jihohin Arewa masu dogaro da tallafin Tarayya.

Bayan taro da kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa, gwamnoni sun bukaci a gyara tsarin VAT don raba kashi 50 bisa fifiko.

Da farko, an tsara cewa za a raba kashi 60 na VAT bisa yawan albarkatun jiha, wanda ya jawo korafi daga wasu gwamnoni.

Kudirin haraji: Sanata Kalu ya shawarci gwamnoni

Sanata Kalu ya ce duk wata jiha a Najeriya tana iya zama mai dogaro da kanta idan shugabanni suka fifita tattalin arzikin jihohinsu.

Ya kara da cewa, gwamnoni su daina sayen motocin alfarma, su mayar da hankali kan abubuwan da za su jawo masu zuba jari.

Kara karanta wannan

"Ban ƙwallafa rai ba": Peter Obi ya canja shawara kan kudurin zama shugaba ƙasa

Kalu ya bayyana cewa kowace jiha a Najeriya na da albarkatu da za su iya zama tushe na dogaro da kai idan aka gudanar da tsare-tsare masu kyau.

Ya ce salon kashe kudade na gwamnonin da manyan jami'an gwamnati yana kawo koma baya ga ci gaban tattalin arzikin kasa, cewar Premium Times.

Kalu ya yaba wa tsarin kudirin haraji

Sanatan ya yi tsokaci kan yadda gwamnonin ke kashe miliyoyin naira kan motoci, maimakon mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa.

Kalu ya jinjina ga tsarin gyaran haraji, yana cewa zai karfafa gasa tsakanin jihohi kamar yadda ake gani a kasashen duniya.

Ya kuma ce akwai dimbin albarkatun kasa a Arewacin Najeriya, musamman ma'adinai da albarkatun gona, wanda za su iya zama tushen arziki.

Kalu ya ce ci gaban Arewacin Najeriya zai samu idan aka jawo masu zuba jari domin amfani da albarkatun da ake da su a yankin.

Kara karanta wannan

Kungiya ta gano sabuwar matsala a rabon harajin VAT, an gargadi gwamnonin Najeriya

Masanin tattalin arziki ya tattauna da Legit Hausa

Lamido Bello ya ce gaskiyar magana ita ce kowane gwamna ya nemo hanyar sama wa jiharsa haraji.

"Dole ne su nemo mafita da hanyar tatsar haraji da zai rika kawo kudin shiga a jihohinsu."

- Lamido Bello

Bello ya ce duba da shirye-shiryen da ake yi na kakaba sabon kudirin haraji, ya kamata su shirya fuskantar abin da ba su so.

Abinci ya fara sauki a Kaduna

Kun ji cewa farashin abinci kamar shinkafa, wake, doya, garri, da taliya sun fara raguwa a kasuwannin Kaduna idan aka kwatanta da tsadar 2024 a Kaduna.

Buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 wanda a baya ake siyar da shi N125,000 zuwa N130,000, yanzu ya ruguzo zuwa N120,000-N123,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.