'Yan Bindiga Sun Koma kan Manyan Ƙasa, An Shiga Har Gida an Ci Mutuncin Matar AIG
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matar wani tsohon mataimakin sufeto janar na 'yan sanda, Hakeem Odumosu a jihar Ogun
- Rundunar ’yan sanda ta tura jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike da nufin kubutar da ita cikin koshin lafiya
- Kwamishinan ’yan sanda ya ba da umarnin amfani da fasahar zamani da kuma tuntuɓar shugabannin tsaro na yankunan Warewa da Maaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Matar mataimakin sufeto janar na ’yan sandan Najeriya (AIG), Hakeem Odumosu (mai ritaya) ta fada hannun masu garkuwa da mutane.
An yi garkuwa da matar tsohon ɗan sandan ne daga gidanta da ke unguwar Arepo, a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Asali: Twitter
Vanguard ta ce wannan mummunan al’amari ya faru ne a safiyar ranar Juma’a, an ce wasu mutane dauke da mugayen makamai ne suka kai hari gidanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun shiga gidan matar tsohon AIG
Maharan sun kutsa cikin gidan suna harbe-harbe ba kakkautawa daga bisani kuma suka yi awon gaba da ita zuwa wurin da ba a sani ba.
Mrs. Odumosu ta tsinci kanta cikin mawuyacin hali na harin masu garkuwa ne yayin da ta ke kokarin shiga gidanta.
Maharan wadanda suka rufe fuskokinsu da abin da ba zai bari a gane su ba, sun ja ta daga motar Lexus Jeep da take ciki, sannan suka tafi da ita ta hanyar jejin da ke cike da kwazazzabai.
Yan sanda sun baza komarsu don ceto matar
Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Ogun, CSP Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ta ce rundunar ƴan sanda ta dauki matakin gaggawa wajen tura dakarunta domin kubutar da matar ba tare da ɓata lokaci ba.
Kakakin ƴan sandan ta ce:
“Mun samu labarin garkuwa da Mrs. Odumosu da ke zaune a titin Aminu a Arepo, kuma ƴan sanda na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da an dawo da ita cikin koshin lafiya.”
Odutola ta ce DPO na yankin ya jagoranci tawagar ’yan sanda zuwa wurin da aka kai harin, inda ake gudanar da bincike mai zurfi a jejin da ke kusa da wurin domin ceto matar.
Ƴan sanda sun fara bincike kan lamarin
Bugu da ƙari, an tuntuɓi shugabannin tsaro na ruwa, ciki har da na Baale Warewa da Baale Maaba domin su taimaka wajen aikin ceton matar tsohon AIG.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Ogun, Lanre Ogunlowo, ya samu labarin abin da ya faru kuma ya ba da umarnin amfani da fasahar zamani wajen binciko inda aka kai matar.
Kakakin ƴan sandan ta ce a yanzu dakaru sun bazama domin ceto matar cikin ƙoshin lafiya tare da daso da ita cikin iyalanta.

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
Ƴan sanda sun tona asirin ƴan ta'adda
Kun ji cewa dakarun ƴan sanda sun kai samame maɓoyar ƴan ta'adda, sun gano masana'antar da ake ƙarawa ƴan tada kayar baya makamai.
Ƴan sandan sun bankaɗo wurin kera makaman ƴan ta'addar ne a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya, kuma har sun kama mutane uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng