Babban Dan Ta'addan da aka Roki Tinubu Ya Sake, Ya Jefo Zargi ga Gwamnati

Babban Dan Ta'addan da aka Roki Tinubu Ya Sake, Ya Jefo Zargi ga Gwamnati

  • Shugaban 'yan a ware na Kudu maso Gabas, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa jinkirin shari’arsa siyasa ce, ba al’amari na doka ba
  • Lauyoyin dan ta'addar sun zargi gwamnatin tarayya da bijirewa umarnin kotu a matakai daban daban a kan shari'a da kama shi
  • A karkashin haka suka yi kira da a sake duba batun gurfanar da Nnamdi Kanu a kotu tare da tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, ya ce jinkirin da ake samu a shari’arsa alama ce ta siyasa a maimakon al’amari na doka.

A taron manema labarai da lauyoyinsa suka gudanar a birnin tarayya Abuja, sun bayyana cewa ana ci gaba da tsare shi ba bisa ka’ida ba, duk da umarnin kotunan gida da na duniya.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu ya zargi gwamnati da rashin adalci. Hoto: Bayo Onanuga|Radio Baifra
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya ce gwamnatin tarayya tana karya dokoki masu yawa, ciki har da kin bin umarnin kotu na sake ba shi beli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin siyasa a jinkirin shari’ar Kanu

Lauyoyin Kanu sun ce tun bayan da suka nemi mai shari’a Binta Nyako ta janye daga shari’ar, babu wata sanarwa daga bangaren gwamnati kan sake tura shari’ar ga wani alkali.

Sun kuma yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta saba umarnin kotunan duniya da ke nuna an take hakkin Kanu da magoya bayansa.

A cewarsu, daga cikin abubuwan da suka faru tun farkon shari’ar a 2015 akwai mamaye gidan Kanu da sojoji suka yi a ranar 10 ga Satumba, 2017.

Lauyoyi sun bukaci belin Nnamdi Kanu

Lauyoyin sun bayyana cewa kin ba wa Kanu beli duk da umarnin kotun koli alama ce ta rashin adalci a kotun da ke sauraron karar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Sun bayyana cewa;

“Yaya za ku yi tsammanin Mazi Nnamdi Kanu ya amince da gurfana a gaban mai shari’a da kotun koli ta gano cewa ba ya adalci?”

Lauyoyin sun yi zargin cewa tun bayan kama Kanu a 2015, an sauya tuhumar da ake yi masa daga batun cin amanar kasa zuwa laifuffukan da suka shafi ta’addanci.

Yadda shari’ar Nnamdi Kanu ta fara

Nnamdi Kanu ya fara fuskantar tuhuma a shekarar 2015 kan laifuffukan da suka hada da cin amanar kasa, hadin baki domin aikata cin amanar kasa da wasu laifuffuka.

A watan Afrilu 2017, an ba shi beli, amma aka soke belin bayan ya bar Najeriya lokacin da aka kai farmaki gidansa a Umuahia, Abia.

Kira na musamman kan yin adalci

Rahoton Trust Radio ya nuna cewa lauyoyin sun nemi a sake duba gurfanar da Kanu tare da tabbatar da cewa kotu ta kasance mai adalci da gaskiya.

Kara karanta wannan

Ana maganar 'Qur'anic Festival', gwamnati ta fito da shiri ga almajiran Najeriya

Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta girmama doka da bin ka’idojin da kotuna suka shimfida wajen tabbatar da adalci ga Kanu da duk masu ruwa da tsaki a shari’ar.

An kashe 'yan a ware 5 a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda da hadin gwiwar sojoji sun yi nasarar hallaka wasu 'yan a ware biyar a Kudancin Najeriya.

Haka zalika rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa sun kwato makamai da dama yayin da suka kai farmaki maboyar miyagun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng