Safarar Mutane: Sama da yaran Najeriya 100,000 sun bace ba labari
A cikin watanni 4 kacal, sama da yaran Najeriya 100,000 ne aka karkata akalarsu daga kasar Libya zuwa kasashen Turai, inda har ya zuwa yanzu ba amo ba labari
A cikin watanni 4 kacal, sama da yaran Najeriya 100,000 ne aka karkata akalarsu daga kasar Libya zuwa kasashen Turai, inda har ya zuwa yanzu ba amo ba labari.
A rahoton da kamfanin dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana, shugaban hukumar yaki da safarar mutane da haramtattun tafiye-tafiye na yankin Benin City, Godwin Obaseki yayi bayanin cewar a halin yanzu ba a san ainahin inda yawancin yaran suke ba a duniya.
DUBA WANNAN: Sanata Ndume: Nayi nadamar goyawa Saraki baya
Obaseki yace, kamata yayi iyayen yara su zamanto masu saka ido da hangen nesa akan masu safarar mutane.
“Daga yanzu, ku gaggauta kai karar duk wani wanda yayi muku alkawarin kai ku ko kai yaran ku Turai ga ‘yan sanda. Saboda a gaskiyar magana wadannan mutane babu inda zasu kai ku face ga halaka, domin kuwa zasu kai ku tsakiyar sahara ne da bakin teku. Ba tare kun ankara ba zaku tsinci kanku a Libya”.
A cewar rahoton, a cikin watanni 6 da suka wuce, kusan ‘yan Najeriya 3,400 ne suka yi bankwana da kasar Libya don dawowa gida Najeriya.
Wasu daga cikin masu gwagwarmayar zuwa Turai ta hanyar bi ta kasar Libiya, suna fadawa hannun miyagun masu tafaucin mutane, inda daga karshe suke rasa rayukansu a cikin sahara ko kuma wurin tsallake tekun bahar Rum.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng