'Yan Bindiga Sun Yi Fitar Dango, Sun Kora Mazauna Kauyen Sakkwato cikin Daji
- An samu rahoton cewa 'yan bindiga sun kai mummunan hari wani kauye a jihar Sakkwato tare da tafka muguwar sata
- Ana zargin 'yan bindiga masu biyayya ga Kachalla Haru da Kachalla Chomo ne su ka shirya harin mai tayar da hankali
- Sun sace mutanen da har yanzu ba a kai ga tattaro adadinsu ba, tare da jikkata wani matashi a kauyen Gado
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - 'Wasu miyagun ‘yan ta’adda sun fantsama kauyen Sakkwato, su ka kaddamar da mummunan hari a kan jama’ar garin.
'Yan bindiga sun farmaki kauyen Gado da ke Unguwar Lalle, karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato da sanyin safiyar Talata.
Zagazola Makama ya wallafa cewa miyagun mutanen sun hargitsa garin baki dayansa, yayin da ake jiran martanin hukumomi a kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun sace mutanen Sakkwato
Miyagun ‘yan ta’adda sun kora mutanen kauyen Gado zuwa dazuka, kuma har yanzu ba a tantance yawan mutanen da aka sace ba.
‘Yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kuma kwashe kayayyakin jama’a ciki har da dabbobi zuwa maboyarsu.
Sakkwato: ‘Yan bindiga sun sun addabi jama'a
Majiyoyin sun tabbatar da cewa maharan sun ji wa wani yaro rauni a lokacin harin kuma sun tilasta wa wasu mazauna kauyen tserewa zuwa dajin Sububu.
Ana zargin wasu gungun ‘yan bindiga karkashin jagorancin Kachalla Haru da Kachalla Chomo, shahararrun shugabannin ‘yan ta’adda da ke aiki a dajin Sububu, da kai harin.
'Yan bindiga sun sace amarya da kawayenta
A baya kun ji cewa an samu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyen Sakkwato a lokacin da ake tsaka da biki, su ka sace amaryar da aka daura aurenta da kawayenta.
An zargi 'yan bindiga da ke mubaya'a ga Bello Turji da kitsa harin, su ka kutsa Kwaren Gamba kusa da kauyen Kuka Teke tare da dauke amaryar da karfin tsiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng