Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta

Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta

- An sace wata daliba ana saura kwanaki biyu a daura mata aure a jihar Kano

- Yarinyar mai suna Amina Gwani Danzarga ta kasance dalibar Kwalejin Tarayya da ke Kano kuma tana zaune a Unguwar Koki

- Baya ga sakonni tes biyu da aka samu daga lambar amaryar, har yanzu ba a ji doriyarta ko ta wadanda suka sace ta ba

Kwana biyar bayan an yi garkuwa da ita, har yanzu ba a san inda wata amarya da za a yi a Kano, Amina Gwani Danzarga take ba.

An tattaro cewa an sace Amina, wacce ke zaune a Unguwar Koki a cikin birnin Kano a ranar Juma'a, kwanaki biyu kafin bikinta.

Ganin karshe da ’yan uwa suka yi wa Amina wacce daliba ce a Kwalejin Tarayya da ke Kano, shi ne yayin da ta fita daga gida zuwa makaranta a yammacin ranar Juma’a.

Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta
Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta Hoto: Food.jumia.com.ng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: 2023: Rashin tabbas yayin da Atiku ke fuskantar yiwuwar hana shi takarar neman kujerar shugaban kasa

Daga baya sai ta ziyarci kawarta a unguwar Dorayi, inda ta ajiye katin shaidar zana jarabawarta.

'Yan uwanta suna zaton an sace ta n e a kan hanyarta ta dawowa daga Dorayi.

Kawun Amina, Gwani Yahuza Gwani Danzarga, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa baya ga sakonnin tes guda biyu da aka samu tun farko daga layin wayarta, dangin ba su samu kira daga yarinyar ba ko kuma wadanda suka sace ta.

“Sa’o’i bayan da aka bayyana cewa ta bata, mun samu sakonnin tes iri biyu, na farko shi ne barazanar kar a sake kiran lambar yarinyar sannan na biyun kuma an tura wa kaninta inda aka nemi su saka ta a cikin addu’arsu domin ana zargin an kasha matar da aka sace su tare.

“Ba mu sake samun wani sako ba saboda lambarta ba ta shiga. Muna addu’ar Allah Ta’ala Ya bayyana duk wanda yake da hannu a wannan satar,” inji shi.

Iyalan sun kuma karyata jita-jitar da ake yadawa cewa wata kila 'yar tasu ce ta shirya hakan saboda ba ta sha'awar auren.

Hajiya Hajara Anas, goggon budurwar da aka sace din, ta shaida wa Daily Trust cewa hakika yarinyar tana matukar son saurayinta, domin ta shiga harkar bikin sosai.

“Tana matukar son saurayinta. A cikin makon da ya gabata, tana gidana don Gyaran Jiki. Na dauke ta zuwa ga makwabciyata da ke Gyaran Jiki a Kofar Mazugal.

Ta kara da cewa "Kun san yarinyar da ba ta son auren ko ba ta son saurayin ba zata yi hakan ba saboda aure."

Saurayin wanda aka sace din, Umar Hassan, wanda har yanzu yake cikin tashin hankali shi ma ya yi watsi da jita-jitar da ake yi cewa matar da zai aura ta boye.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa

“Na san wacece Amina; yarinya ce mai nutsuwa da biyayya. Ba za ta iya yin wani abu da ya saba wa addininmu ba. Muna kaunar junanmu kuma dukkanmu muna da sha'awar ganin ranar aurenmu,” inji shi.

Yayin da yake tuna ganawarsa ta kashe da ita kafin nemanta da aka yi kuma aka rasa, Umar ya ce, “Ina cikin tuki na kira ta amma lambarta bata shiga ba, sai daga baya ta kira ni kuma muka shiga tattaunawa a kan shirye-shiryen auren namu amma saboda rashin ‘sabis’ sai na yi alkawarin kiranta da zarar na samu dama.”

“Bayan na dawo gida da misalin karfe 11.00 na dare, sai na kira layinta amma ban samu ba, saboda haka ban kawo komai a raina ba face matsalar rashin ‘sabis’.”

“Washe gari na sake kiranta amma layinta bai shiga ba. Sai na kira wani yayanta wanda ya labarta min abin da ke faruwa yana kuma bani hakuri tare da rarrashi a kan kada na tayar da hankali kawai na dage da addu’a,” in ji shi.

A halin yanzu, kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya ci tura, saboda lambar wayar Jami’in Hulda da Jama’ar ba ta je ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta Zamfara ta sake sauya jami’inta na 'yan sanda (DPO) da ke Kaura-Namoda, sakamakon zargin da ake yi masa da hada baki da ‘yan bindiga da ke addabar yankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Mohammed Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai, a Gusau a ranar Litinin.

Ya kuma bayyana cewa, Kwamishinan 'yan sanda, Mista Abutu Yaro ya sauyawa DPO na yankin wurin aiki zuwa hedikwatar 'yan sanda a matsayin OC Provost, yayin da aka nada ASP Umar Abdullahi a matsayin DPO na yankin.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel