'Abin da Ya Sa Muka Cafke 'Dan Jarida Mai Binciken Kwa Kwaf': Sojoji Sun Wanke Kansu
- Rundunar sojojin Nigeriya ta bayyana dalilin tsare wani sananne kuma matashin dan jarida mai suna Fisayo Soyombo
- Mutane da dama da kungiyoyin fararen hula sun bukaci rundunar ta yi gaggawar sakin dan jaridar mai binciken kwa-kwaf
- Hakan ya biyo bayan kama Soyombo a wurin wasu miyagu da ake zargin suna fasa bututu da safarar mai ba bisa ka'ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rundunar sojojin Nigeriya ta yi magana bayan korafi da ake yi kan cafke dan jarida mai binciken kwa-kwaf.
Rundunar sojojin ta tabbatar cewa dan jaridar mai suna Fisayo Soyombo yana hannunta kamar yadda ake yadawa.
Sojoji sun magantu kan cafke dan jarida
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin X a yau Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin daraktan hulda da jama'a, Laftanar-kanal Danjuma Danjuma ya fadi dalilin rike dan jaridar.
Danjuma ya ce lamarin ya faru ne bayan samun bayanan sirri game da barayi masu fasa bututun mai a yankin.
Ya ce an cafke Soyombo da wasu mutane a wurin da ake zargin miyagun, yanzu haka ana kan bincike game da lamarin.
'Dalilin kama dan jarida a Rivers'- Sojoji
"Za ku iya tunawa rundunar sojoji ta kara kaimi wurin dakile masu fasa bututun mai da safarar mai babu ka'ida kuma tana samun nasarori."
"Mun samu bayanan sirri kan wasu miyagu masu fasa bututun mai da safarar mai babu ka'ida inda muka kai musu samame."
"Yayin samamen, an kama wasu mutane da dama cikin har da dan jarida mai suna Fisayo Soyombo."
"Yanzu haka ana kan bincike, kuma an kama Soyombo ne saboda alaka da masu fasa bututun mai, ya kamata yan jaridu su rika bincike kafin yada labarai."
- Laftanar-kanal Danjuma Danjuma
Sojoji sun hallaka 'yan Biafra
Kun ji cewa Rundunar sojin Najeriya ta yi arangama da yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biafra a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo kuma sojojin Najeriya sun kashe da dama daga cikin 'yan ta'addar yayin fafatawar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng